Blogger


Blogger shi ne mutumin da yake rubuce-rubuce a kan al’amuran yau da kullum da suka shafi rayuwa a shafukan yanar gizo. Za ka iya zama cikekken ‘blogger’ idan ka mallaki website, ko blogsite a Google Blogspot da Wordpress da sauransu, ta manhajojinsu ko kuma shafukansu.


• GOOGLE BLOSPOT

Wesbsite: blogspot.com

Android App: bit.ly/3IPObaQ

iSO (Apple): bit.ly/3IPOzGk (unavailable/an cire shi)


• WORD PRESS  

Website: wordpress.com

Android: bit.ly/3cjsrb7 

iSO (Apple): apple.co/3REi41F


AMFANIN BLOG


1. Neman kudi 

Idan ka buÉ—e shafi a Google Blogspot.com kana iya samun kamar 300 visitors a kowacce rana, yawan samun waÉ—annan traffic zai baka damar É—ora tallace-tallace (ads) za su (iya) biyan ka miliyoyin kuÉ—aÉ—e a duk watan duniya.


2. Wallafa (Publishing)

A matsayin FREELANCER, za ka iya amfani da blogsite, domin wallafa rubutunka, ba tare da kana biyan so sisi ba.


3. Tallace-tallace

Ana iya tallata kaya ta blogsites kyauta, kamar a website. 


MATAKIN BUÆŠE BLOG PLATFORM(S)


• GOOGLE BLOGPOT


1. Ka mallaki email

Idan da Blogspot za ka yi amfani wajen buÉ—e blogsite, da GMAIL kaÉ—ai ake amfani. 


2. Ka buÉ—e ‘app’ (Blogger) ko shafin blogspot.com.


3. Sai ka sa GMAIL naka wajen SIGN-IN.   


4. A shafin farko na Blogspot, za ka ga CREAT YOUR BLOG, sai ka shiga.


5. sai ka saka PAGE TITLE (misali SAMPLE USER), sai ka yi NEXT.


6. Za ka zaÉ“i URL (sunan shafi), misali ‘usersampling.blogspot.com’ [idan akwai mai irin wannan URL din, za su ce ma, “SORRY, THIS BLOG ADDRESS IS UNAVAILABLE” ko “INVALID OR NOT SUPPORT” (idan ka yi amfani da wasu symbol, ko Kalmar da bata dace ba)], sai ka NEXT.


Shikenan, ka mallaki shafin blog da Google Blogspot. 


• WORDSPRESS


1. Ka yi amfani da email. 

Idan kuma da Wordpress ne, za ka iya amfani da kowanne irin ‘email account’ (Gmail, Yahoo Mail, Hotmail…).


2. Ka buÉ—e ‘app’ (Wordpress) ko shafin wordpress.com.


3. Idan ta website ne (wordpress.com), ka shiga GET STARTED ko START YOUR WEBSITE. Sai ka sa EMAIL, USERNAME da PASSWORD, za su tura ma CONFIRMATION ta EMAIL.


Idan ta ‘app’ ne, za ka shiga LOGIN OR SIGN UP WITH WORDPRESS. Sai ka sa EMAIL, ka danna CONTINUE. za su tura ma CONFIRMATION ta EMAIL.


4. Ka bu ɗe EMAIL, ka bu ɗe saƙon WORDPRESS ta inbox, sai ka pressing kan SIGN UP.


5. Idan a ‘app ne’ za zaÉ“i topic (misali, Food, Lifestyle, News, Personal, Photography…), ko kuma ka yi SKIP.


6. Za ka zaɓi THEME, sai ka CHOOSE.


7. Za ka zaɓi sunan DOMAI, misali, digitalusersample.wordpress.com.


8. Za su buÉ—e ma shafi YOUR SITE HAS BEEN CREATE, sai ka pressing OK


WALLAFA A BLOGSITE

Hanya mafi sauÆ™i ta yin publishing a BLOGSITES it ace, yin amfani ‘apps’ (Blogger/Wordpress) ko kuma ta computer (da browser).


Akwai sauran sites da za ka iya blogging da su kamar Wix.com, Medium.com, Weebly.com da sauransu.


✍️Aliyu M. Ahmad

17th Dhul-Hijjah, 1443AH

16th July, 2022CE


#AliyuMAhmad #FasaharZamani #Blog #Blogger #Wordpress








Post a Comment

0 Comments