Na sha gwada wannan laƙanin a lokuta da dama, kuma Alhamdulillah, yana min aiki sosai.
A duk lokacin da ka shiga cikin damuwa, ka ruɗe, al'amuran duniya sun harɗe ma, ka rasa mafita...kawai ka yawaita ISTIGFARI.
• Astaghfirullah
• Astaghfirullah wa atubu ilaih
• Astaghfirullah hal 'azimal lazi laa ilaha illa huwal hayyul ƙayyum wa atubu ilaih
Da wasu lafuzzan na Istighfari da suka tabbata a sunnah... ka ɗauki ɗaya, ka yi ta yi, kana maimaitawa, za ka sami nutsuwa, mafita, da aminci daga abin da yake ba ka tsoro.
Abdullahi ibn Abbas رضي الله عنه Ya ce, Manzon Allah ﷺ Ya ce: "Duk wanda ya lazimci istighfari, Allah zai kawo masa budi a cikin kowanne bakin ciki, da kuma mafita a kowanne kunci, sannan ya azurta shi da inda ba ya tsammani" [Abu Dawud, 1518 & Ibn Majah, 3819].
Astaghfirullah!
✍️Aliyu M. Ahmad
1st Muharram, 1444AH
30th July, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari
0 Comments