Abokina Ka Rike Sana'a

 



Abokina Matashi!


Idan wani ya ce ka FIYE NEMAN KUƊI, don kana neman rufawa kanka asiri; ka lissafa masa expenses na kwana ɗaya (3 meals, cleansing kits, trans, subs...), ka ce za ka zauna a gida, ya biya ma buƙatunka na kwana ɗaya ma kawai.

Abokina!

Ka tashi ka nemi sana'a, za a ce ma,

"ka fiye naci"
"kana jin jiki, shi ya sa ka kama sana'a"
"gari ne ya fara ma zafi"
"ka dage da neman kuɗi..oh"

Ka rubuta ka ajiye, masu yi ma waɗannan maganganun kashe gwuiwa, idan ka kafu, sune masu zuwa karɓar bashi, ko neman taimako.

Abokina!

Gaskiya magana, ba wani mai taimakonka, THIS LIFE IS 100% YOUR RESPONSIBILTY, KAI ZA KA TAIMAKI KANKA. Don ka yiwa (wani) ɗan siyasa campaing, ba ya nufin sai ya nema aiki. Project ne na campaing, kuma an baka kuɗin data (a lissafin ƴan siyasa).

Don uncle yana Director a Abuja, ko wani babban yaya na kasuwa, babu mai haƙƙi na dolen-dole sai ya baka kuɗi ko aiki, KYAUTATAWA IN SUN YI NIYYA. Ka fara taimakon kanka, tukun SAI SU TALLAFA MA.

Abokina!

In baka da sisi, ko sadaka ake nema a cikin masallaci, sai dai a wuce da akwatin Fisabilillah ta gabanka kana susar kai, baka iya sa hannu a aljihu.

Manufar sana'a ita ce, samun kuɗin rufa kai asiri, biyawa kai bukatu na dole (abin ci, muhalli, lafiya, ilimi, sutura...), nesanta kai daga wofantar da daga roko ko dogara da wani. Ba wai a tara 'luxuries" aka taƙama da fankama ba.

Waɗannan manyan motoci, da danƙareran gida, da manyan rigunan da kake sha'awa, kafin a same su, sai da aka yi gumi, aka sha gwargwarmaya. Kai ma ka tashi ka nema, Allah zai baka fiye da wannan in Ya ƙaddara. Ba mai ɗaukar ƴarsa ya ba ka, ba ka da kuɗi, ba ka da sana'a.

✍️ Aliyu M. Ahmad
30th Dhul-Hijjah, 1443AH
29th July, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments