iPhone14 na dab da shigowa kasuwa, kuma da alama kuɗinta zai yi sauƙi sosai, ana PREDICTION, za ta fara daga $1199, akwai 14, 14 Pro, 14 Pro Max da 14 Max.
Matsalar, ba ka siya ba, wata shekarar ka zama tarihi, iphone 15 ce zata fito, ita kuma ta hannunka (14) darajarta ta karye. Idan kana da iPhone 13, da zarar 14 ta fito a ranar 14 ga Satumba, 2022; ka koma ajin baya. Idan kana da 12, ka koma ajin baya-baya. Idan iPhone 11 kake da, ka koma ajin bayan-baya... Sorry to the family 😔
Kar ka bari ruɗin canja waya don trending, da son burge mutane ko 'yan mata, ko gasa da abokai... ya hanaka tsinanawa kanka abin kirki. Ka mallaki waya don buƙatar kanka kawai. Har yanzu, wasu (mutanen) ba sa iya bambance 11 kake riƙe da, ko 12 ce ko 13... kai kuma sai hura hanci kake, ka rike wayar ₦300k+ - ₦500k+.
Shekarar da ta wuce, iPhone 13 Pro Max, har 1mil+ ake siyanta, amma yau sabuwarta ma a kasuwa bata wuce ₦700+ ce, za ka iya samun Dubai ko London Used a ₦600k - ₦650k; kusan 50% (i.e. ₦500k) ya zabge daga tsohon farashinta. Yi tunani! Da wata ƙadara ka siya ta ₦500k last year, fili, ko gona, ko wani abu mai daraja (gold, diamond, kayan abinci...), ko hannun jari (stocks)... ya darajar ƙadarar zai kasance a yau?
Yanzu idan da VIVO 'yar ₦7k na yi posting ɗin nan, ba wanda ya sani, idan da iPhone 13 Pro Max ma na yi, duk dai abu ɗaya za ku gani... ko a Twitter da ake Source Label (for iPhone, Android ko Desktop), da mai iPhone 5 (ta ₦25,000), da mai 13 Pro Max ta ₦750,000, duk label ɗaya ne.
iPhone a hannunmu, yawanci bata wuce CAMERA da DARAJA... Google Pixel ma, gani nake, tafi min iPhone ɗin camera da cire portrait, kuma kudinta bai ma kai na iPhone ɗin ba 🖼.
Allah Ya ƙara rufa mana asiri.
✍️Aliyu M. Ahmad
19th Dhul-Hijjah, 1443AH
18th July, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #FasaharZamani #iPhone

0 Comments