Wakokin Hiphop



Yawancin a waƙoƙin Hip Hop, Afrobeats da Pop da za ka ji kalmomin batsa, da saɓo, da shirka, har ana Taslisin Ubangiji (a wasu)... amma a haka za ka ji wani ya kunna yana maimaita kalmomin da bai ma san ma'anarsu ba, yana bi (mimic), ko har yana tiƙa rawa.


Ta ya kake tunanin samun nutsuwa da sautin da ake yi wa Ubangijinka shirka ko ambatar kalmomin saɓo da na batsa?

Ka gwada searching a Google na sunan waƙa, ka ƙara LYRICS a gaba, ka duba kalmomin (lyrics) da ake waƙar da su.

IGNORANTIA JURIS NON EXCUSAT
Gaskiya ya kama mu faɗaka!

✍️ Aliyu M. Ahmad
4th Shawwal, 1444AH
2nd August, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments