Dare da rana kana neman kuɗi, ko a wata ne, ka ɗan rika karya ƙashin kaza, ka sami irin farfesu (dabge) nan, ko dandum kaza, ko kilishi, soson kwai... alkubus, alkaki da zuma, nakiya, tuwon madara... burger, donuts, ice cream, pizza, falafel...
Idan kuma ka so neman albarka, ka je kasuwa ka samo kaza, ko kifi (manya-manyan karfasa ko dankwaso), ka kawowa Umma ko uwargida (iyali) a rababbaka, kowa a ɗanɗana a gida ana sa ma albarka, in ka so, ka haɗo da fruits 🍒🍇🍍🍌, a haɗa ma cocktails, ko fura da nono.
Amma kullum kana kan keken ɗinki, leburanci, ko yawo a rana, ko yini cikin kasuwa ko shago/office... Kar ka yiwa kanka mugunta, ban kuma ce kullum ba, amma a ƙalla dai a sati (weekly) ko a wata (monthly) sau ɗaya dai, ka tsinka miyau, ka ci guminka, ka ji yadda elites ke ji.
Allah Ya ƙara azurta mu daga falalarSa, amin.
✍️Aliyu M. Ahmad
3rd Muharram, 1443AH
1st August, 2022CE
#AliyuMAhmad #Sanaa
0 Comments