HANKALI DA ADDINI (MUSULUNCI)
Hankali
(mind/العقل); shi ne dama Ubangiji (Allah) ya yiwa ɗan
Adam na tantance abun da suke daidai/dace da wanin haka (rashin hankali/hauka)
ta hanyar ilimi (epistemic), tunani (thinking/التفكر), bincike (researching/البحث)
da bibiyar al’amura daban-daban da suka shafi rayuwarsa ta yau da kullum, kama
daga addini, mu’amala da nazari cikin halittu domin tabbatar da wani abu, ko
kore shakku.
Wannan
dalili yasa babu wani addini (Musulunci ko waninsa), ko tsarin mulki (أحكام
السلطانية) ko ƙasa (ta Musulunci, ko ta Musulmai ko Secular) da suka
bawa wani abu muhimmanci fiye da hankali. Duba da ɗorawa
mabiyin addinin wani nauyi (تخليف) na wata bauta (ie. Sallah, Azumi, Aikin
Hajji dss), jagoranci al’umma (shugabanci), shiga mu’amala (kasuwanci,
yarjejjeniya, wakilci). Saboda hadisi Shugaba (S.A.W.):
رفع
القلم عن الثلاث: الصبي حتى يبلغ، والمجنون حتى يفيق ، والنائم حتى يستقيظ
]الترمذي،
النسائي وإبن ماجه[
Wannan
zai nuna maka muhimmancin da addini (Musulunci) ya bawa hankali; shi yasa babu
wani nauyi da addini (Musulunci) ke ɗorawa kan wanda babu hankali a tare da shi (e.g. yaro, mahauci da
mai bacci), domin sai da hankali mutum zai fahimci Sharia.
Haka
nan, babu wani abu da dokar addini ko ƙasa take karewa da martabawa fiye hankali, idan har kayi duba
na-nutsuwa cikin kowannen tsarin doka walau dinan ko zamanan zaka tarar tana da
alaƙa da
bawa hankali kariya; misali haramta shan kayan maye (Intoxication/السخرية) (Ma’ida:
90-91), haramta duk wani abu da zai tadawa ɗan Adam hankali ko takurawa tunaninsa (nuisance/إزعاج) (Shura:42),
haramta duk wani abu da ya saɓa da al’adar hankali (bokanci, sihiri/witchcraft/السحر) (Baqara:102),
tsoratarwa (intimidation/التخويف), fushi (Anger/غضد) dss.
Sannan
idan ka ji an kawo wata aya a cikin Alkur’ani Maigirma, wacce take ɗauke
da wani babban muhimmin saƙo ko nuna aya cikin manya ayoyin/halittun Allah sai kaji an ce maka
WANNAN AYACE GA MASU HANKALI; misali: Baqara: 164, Aal-Imran:
190, Yusuf: 111, Ar-Ra’d: 19,Ibrahim:
52, Hajj: 46, Yasin: 62, Sad; 29, Zumar: 9 &
21, Jathiya: 5, Hadid, 17 dss.
Cikin
ni’imar Allah, Allah Ya banbanta ɗan Adam da wasu halittu (dabbobi) da matakin hankali (mind/العقل)
da tunani (thinking/التفكر). Wanda da ba don hankali ba, da mu mutane (Ƴan
Adam) da dabobbin duk ɗaya muke babu banbanci, saboda akuya ma tasan idan tana jin yunwa
ta ci abinci, idan ta fita daga gida tasan hanyar dawowa, ta san uwarta da
danginta, kai har in ka dake tama ta kan jin zafi, idan ta ji matsuwa (fitsari
ko bayan gari) ta ɗan sukunya ta yi, idan ta ji sauti na tsoro ko ta ga wani abu mai
cutarwa (kamar kura) zata razana ta gudu, idan ta ji ƙamshin
dusa ko ciyawa takan sha’awi
ta ci, har idan sha’awarta
ta tashi (sexual desire/craving) takan nemi a biya mata buƙatarta.
A ƙoƙarin
Addinin Musulunci na kare martabar hankalin dan Adam; An ruwaito hadisi daga
Nana A’isha (R.); Ta ji Shugaba (S.A.W.) Yace:
"إذا
وضع العشاء وأقيمت الصلاة فابدءوا بالعشاء"
Ba
wai don cin-abinci ya fi Sallah muhimmanci ba ne, a’a sai don kar ka je Sallah
hankalinka ya rabu biyune. A wata
ruwayar ma ta Hassan ibn Ali ibn Abi Talib (R.), idan har mutum na da
kokwanto cikin wani abu, to ya koma ya kama abin da babu kokwanto a ciki:
Shugaba (S.A.W.) Yace:
"دع ما يريبك إلى ما
لا يريبك"
Sannan
yadda Ubangiji (SWT) ya kaddara aikin harshe jin ɗanɗano
(taste/الطعم), idanu kallo (sight/البصر), kunne jin sauti (hearing/السمع),
sai ya halittan mana zuciya da kwakwalwa domin mu riƙa
tunani (thinking/التفكر) da nazari/tadabburi da hankalin da ya bamu, ya
kuma sanya mana ambatonsa (الذكر) abinci ga zukatanmu domin kwantarwa da ruhi
hankali da samun nutsuwa (الطمانينة) (Raad:28).
Na san wani zai iya tambayar kansa; shin ko menene fa’idar wannan
rubutu mai yawan maimaituwar wannan kalma ‘HANKALI’?
Don
ka cirewa zuciyarka cewa babu wani abu da Addinin Musulunci zai kawo maka na
tsare-tsarensa (Sharia) kace wai SHARIA TA SABAWA HANKALI, sai dai kace
ILIMI SABANIN JAHILCI (shawara kurum kayi karatu).
خير الكلام من قل ودل. سبحانك اللهم وبحمدك، أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك
وأتوب إليك.
28th Dhul-Qa’adah, 1438AH
(Sun. 20th August, 2017CE)
1 Comments
Muna fa'idan tuwa da rubututtukan ka Allah ya saka da alkhairi
ReplyDelete