Aikin Gwamnati


Ɗaya daga cikin abin da ya kamata al'ummarmu su sauya tunani a kai; raba tsakanin AIKI da SANA'A (DOGARO DA KAI), kalmomi ne, amma suna da tasiri a rayuwarmu ta yau da kullum. A wajen mutane da yawa, AIKI, shi ne aiki mai albashi (salary) a ma'aikatar gwamnati, ko private sectors, kamar banki, kamfani ko NGOs. SANA'A kuma, dogaro da kai, kasuwanci ko sana’ar hannu (skills).

Aikin gwamnati kala biyu ne a Nigeria, civil service (aikin ofis a ƙarkashin ministries) da public service (sune aiki tsaro: police, armed forces da paramilitary). Aikin gwamnati ‘security’ ne kamar yadda ake faɗa, saboda a duk ƙarshen wata kana da yaƙini za a baka albashi.

Idan baka da lafiya, za a yi ma uzurin fita wajen aiki, kuma za a baka albashinka. Za ka (iya) samun lamunin gini (mortgage) a tsarin NHF, za ka iya karɓar bashin mota ko babur (car/vehicle loan), ko bashin kayan abinci, sai a rinƙa raga daga albashinka duk wata. Akwai waɗanda suke mallakar gida da abin hawa ta wannan tsari. Za a rinƙa ma promotion lokaci-lokaci. Ida kuka yi wani aiki na musamman kuma, ko zuwa wajen wani taro, za a biya alawus. Kuma, za a iya korarka, ko dakatar da kai kan saɓa wata ƙa’idar aiki.

Aikin gwamnati yana da tsarin gratuity da pension. A gratuity za a rinƙa ciran wani percent daga albashinka ana ajiye ma a tsawo lokacin aiki, bayan ka yi ritaya, a baka ‘lump-sum” (baki ɗaya), ko lokaci-lokaci bisa tsarin CPS ko DBS na Pension Reform Act (2014).

Shi kuma mai sana’a: kasuwanci ko aikin hannu (skill work), yana samun kuɗin shiga gwargwadon aikinsa ko juya kasuwa. Yana samun ci gaba gwargwadon gudanar da sana'arsa.

Da aikin gwamnati da sana’a duk halastattu ne a addini. A addinance, dole ne akan kowanne mutum ya fita nema daga falalar Allah, ta halastacciyar sana'a don rufa kai asiri. Kamar Annabi Yusuf da Harun عليهما السلام ma’aikatan gwamnati ne, wasu daga cikin Annabawa sun yi kiwo, noma, su, da fatauci, wasu kuma sassaka, saka, gini da sauransu.

Kalmomin AIKI da SANA’A na shafar mutune da yawa, har wani yana jin ƙasƙanci, hatta a WAJEN NEMAN AURE, akwai gidajen da in ba aikin gwamnati ko aiki mai albashi kake ba, ba za su baka aure ba, sai dai in ka kai Alhaji, sai dai ka ji ana ce wa ai ba shi da aiki, ko bai samu aiki ba.

Irin wannan ɗaukaka aikin gwamnati ya sa wa matasa da yawa tunanin bautar ofis. A halayar zamantakewa kuma, al’umma sun fi ƙoƙari samun conformity (abin da aka fi ɗaukakawa). Misali, da maza suka nuna sun fi son farar mace, sai ‘yan mata da yawa suke bleaching don su sami karɓuwa.

A hankalce, ba wani halastaccen aiki da yake ƙasƙanci, da GAREJI, da OFFICE, da BAKIN HANYA, da SHAGO... duk wajen neman rufawa kai asiri ne (manufar kenan). Akwai wanda zai yi arziki da noma ko kasuwanci, har ya zama misali, wani da aikin sufuri, gidan abinci… kamar yadda wani zai sami ɗaukaka a aikin gwamnati. Idan kana buƙatar aikin gwamnati, MATASHI; ka riƙe sana'a, kafin Allah Ya kawo ma aikin da kake mafarki. 

Ka riƙe sana'arka, kar ka ji ƙasƙanci, cikin sana'a ma akwai rufin asiri. Yawancin masu karɓar bashi a hannun 'yan kasuwa da bankuna ma'aikatan gwamnati ne, masu jiran albashin ƙarshen wata, ba kamar mai sana'a ba, wanda kullum yana samu daga falalar Allah. Kuma ka duba misali, daga cikin waɗanda suka yi graduation na sakandire, daga 2010 zuwa yau, idan ka duba da kyau, yawancin waɗanda suka mallaki gida, suke da aure a yau, ba ma'aikatan gwamnati ba ne.

--------------------------------------
• Rubutu mai alaƙa 👉 bit.ly/3PC0Kbz
--------------------------------------

✍️ Aliyu M. Ahmad
24th Muharram, 1444AH
22nd August, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Sanaa

Post a Comment

0 Comments