CIWON SO!

Ciwon So!
Yana daga cikin jarrabawa mafi girma da Ubangiji zai yiwa bawa a duniya, shi ne ya jarrabe shi da soyayya.

Idan aka ambaci kalmar soyayya, wasu na mata fassara da jin dadi, kulawa, kwanciyar hankali; amma a dayan bangaren akwai azaba.

Idan zaka so, a so ka, hakika akwai ni'ima da jin dadi, amma da zarar kai ne ke yin soyayya, amma idan ya kasance masoyinka na son wani daban (kana son maso-wani), a nan zaka dandana azabar rayuwa.

Kar ka yiwa wanda ya shiga irin jarrabawa dariya, domin jinya ce (ba'a yiwa motar gawa dariya). Idan ciwon so ya kama mutum, komai girman sa, iliminsa, izzarsa, dukiyarsa... bai isa sarrafa kansa, face SO ne ke sarrafa shi.

So tamkar kayan maye yake, domin wanda ya sha kayan maye ba shi da karfin ikon sarrafa kansa. So cuta ne, cuta da take kama zukata da tunani (مرض نفسانى), cuta ce dake sanya wasiwasi, rashin nutsuwa (wani lokacin) tare da bautar da zukata da gangar jiki [روضة المحبين, shafi na 255].

Idan mutum na sonka, kai ne likitan shi da zaka warkar masa da cutar so. Kar ka cutar da shi. Idan baka da ra'ayinsa, ka hanzarta sanar da shi cikin kalaman likita-da-majinyaci, kar ka rataye shi, ya dau tsawon lokaci, domin cikin so, akwai hisabi. 

Ke kuma zuciyar da so ya buga, ki yi hakuri da jarrabawa so, matukar an ki miki tarba, ki karbi kaddara, domin jarrabawa ce.

Ku tausayawa wanda ciwon so ya buga, ba abin dariya ba ne, cikin maza ko mata, Allah Ya hada kowa da mai kaunarsa.

Aliyu M. Ahmad
6th Dhul-Qa'adah, 1443AH
6th June, 2022CE

Post a Comment

0 Comments