𝗦𝗛𝗔𝗬𝗘-𝗦𝗛𝗔𝗬𝗘 💊💉🍻


Idan al'umma ba su tashi tsaye wajen yaƙar 𝗦𝗛𝗔𝗬𝗘-𝗦𝗛𝗔𝗬𝗘 ba, ina tausayawa goben ƴaƴanmu, da makomar al'ummarmu.

Ta'amulli da miyagun kwayoyi da sauran kayan maye, 𝘀𝗵𝗶 𝗻𝗲 𝗺𝗮𝘁𝗮𝗸𝗶𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗸𝗼 𝗱𝗮 𝗺𝗮𝘁𝗮𝘀𝗵𝗶 𝗸𝗲 𝗿𝘂𝘀𝗮 𝗿𝗮𝘆𝘂𝘄𝗮𝗿𝘀𝗮 𝗯𝗮𝗸𝗶 ɗ𝗮𝘆𝗮, kuma yana da wuyar saituwa. saboda 'addiction'. A ƙarshe, 𝗯𝗮 𝘇𝗮𝗶 𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝗸𝗮𝗻𝘀𝗮 𝗯𝗮, 𝗯𝗮 𝘇𝗮𝗶 𝗶𝘆𝗮 𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝗸𝗼𝘄𝗮 𝗱𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮𝗶 𝗯𝗮, sai dai ma ya cutar da duk waɗanda suke tare da shi. 

Mai shaye-shaye in ya rasa kudin siyan abin shan nan, bai ƙi ya yiwa kowa 𝘀𝗮𝘁𝗮 ba, ko ma na mene ne, don ya biya buƙatarsa. Shi ya sa, kar ka yi mamaki ganin ƙaruwar masu ƙ𝗮𝗿𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗺𝗮𝘀𝘂 𝗸𝘄𝗮𝗰𝗲𝗻 𝘄𝗮𝘆𝗮, 𝗴𝗮𝗿𝗸𝘂𝘄𝗮 𝗱𝗮 𝗺𝘂𝘁𝗮𝗻𝗲, 𝘀𝗮𝘁𝗮𝗿 𝗮𝗯𝗶𝗻 𝗵𝗮𝘄𝗮, ɓ𝗮𝗹𝗹𝗲 𝘀𝗵𝗮𝗴𝘂𝗻𝗮... Yawancin waɗanda ake kamawa da irin waɗannan laifuffukan, zaka ga suna ta'ammuli da 𝗸𝗮𝘆𝗮𝗻 𝗺𝗮𝘆𝗲.

Kuma yau, ko kai ne kake shaye-shaye, baka da ikon hana kanka cikin sauki, 𝘀𝗮𝗶 𝗶𝗻 𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵 𝗬𝗮 𝘀𝗼 𝗸𝗮 𝗱𝗮 𝘀𝗵𝗶𝗿𝗶𝘆𝗮, saboda '𝗮𝗱𝗱𝗶𝗰𝘁𝗶𝗼𝗻' din nan. Kayan mayen ke sarrafa su, ba su ke sarrafa kayan mayen ba. Ga wanda ya yi nisa, ba watsar da shi za a yi ba, akwai matakan daidaita halayya na '𝗮𝗱𝗱𝗶𝗰𝘁𝗶𝗼𝗻 𝗿𝗲𝗰𝗼𝘃𝗲𝗿𝘆'.

Iyaye a matakin farko, a rika lura da abokanka da yara ke abota da su, wuraren da suke tafiya yawo. In babu makaranta, yaro ya kasance yana wajen koyon sana'a, ko yana gida. Da yawa a wajen abokai ko yawon sharhoyila ake koyowa. 𝗠𝗔𝗜 𝗦𝗛𝗔𝗬𝗘-𝗦𝗛𝗔𝗬𝗘 𝗕𝗔 𝗪𝗔𝗡𝗗𝗔 𝗬𝗔 𝗙𝗜 𝗖𝗨𝗧𝗔𝗥𝗪𝗔 𝗞𝗔𝗠𝗔𝗥 𝗜𝗬𝗔𝗬𝗘𝗡𝗦𝗔.

Allah Ya shiryar mana zuri'a.

✍️ 𝗔𝗹𝗶𝘆𝘂 𝗠. 𝗔𝗵𝗺𝗮𝗱
19th Dhul-Qaadah, 1443AH
19th June, 2022CE

Post a Comment

0 Comments