FATAWAR SOYAYYA (1): INA SO, BA A SONA

• TAMBAYA:
Ya za a yi na shawo kanta? Ina tsananin sonta, amma ta furta min bata sona.

• AMSA:
Jarrabawa ce! Duk wanda ya ce baya sonka, ya hutar da kai, domin ya fitar da kai daga rataya da igiyar zato. Idan ka ci gaba da neman sai ya soka, duk kyautatawa da kulawa da zaka ba shi, zaka ci gaba da wahalar da kanka, kuma kai ka so.

Zig Ziglar (1923 - date) a MotivationalHub, ya ce: "A clear rejection is always better than a fake promise." Ma'ana: "A nuna ba a sonka kai tsaye, ya fi a rataye ka a igiyar zato."

Shaykh al-Islam Ibn Taymiyah رحمه الله (h. 661 - 728) yake cewa: 

فأما إذا ابتُلى بالعشق وعف وصبر فإنه يثاب على تقواه لله

“Duk wanda aka jarraba da soyayya, in har ya kiyaye mutuncinsa, ya yi hakuri, Allah zai ba shi ladan taqwa...” [مجموع الفتاوى، 10/133].

SOYAYYA ITA CE, KA SO; A SOKA. DUK WANI BAYAN WANNAN, AZABA CE!

✍️ Aliyu M. Ahmad 
13th Dhul-Qaadah, 1443AH
13th June, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Soyayya

Post a Comment

0 Comments