Kafin na fara magana akan alfanun Gmail, zan so mu ɗan fahimci '𝗲𝗺𝗮𝗶𝗹' a taƙaice.
Email, kalmomi ne guda 2 aka haɗe a waje ɗaya (𝗰𝗼𝗺𝗽𝗼𝘂𝗻𝗱𝗶𝗻𝗴), e- (𝗲𝗹𝗲𝗰𝘁𝗿𝗼𝗻𝗶𝗰/𝗱𝗶𝗴𝗶𝘁𝗮𝗹) da kuma '𝗺𝗮𝗶𝗹' (saƙo), ma'ana, '𝗲𝗹𝗲𝗰𝘁𝗿𝗼𝗻𝗶𝗰/𝗱𝗶𝗴𝗶𝘁𝗮𝗹 𝗺𝗮𝗶𝗹' (saƙo da ake iya aikawa ta hanyar sadarwar zamani). Sai aka taƙaice '𝗲𝗹𝗲𝗰𝘁𝗿𝗼𝗻𝗶𝗰' zuwa '𝗲-'. '𝗲-' na nufin, duk wani abu da za a yi, ta hanyar amfani da sadarwar zamani; akwai 𝗲𝗺𝗮𝗶𝗹, 𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸𝘀, 𝗲-𝗰𝗼𝗺𝗺𝗲𝗿𝗰𝗲, 𝗲-𝗹𝗲𝗮𝗿𝗻𝗶𝗻𝗴 da sauransu.
Ana iya rubuta shi a '𝗲-𝗺𝗮𝗶𝗹' ko '𝗲𝗺𝗮𝗶𝗹', ma'ana da '𝘀𝗮𝗿ƙ𝗲' (𝗵𝘆𝗽𝗲𝗻), ko babu 𝘀𝗮𝗿ƙ𝗲 (a haɗe), duk daidai ne a ƙa'idar rubutu (Marko, 2016).
Gmail, '𝗲𝗺𝗮𝗶𝗹 𝗽𝗿𝗼𝘃𝗶𝗱𝗲𝗿' ne da ake amfani da shi wajen aika saƙo ko rijistar wasu shafuka a kafar sadarwa kamar sauran '𝗽𝗿𝗼𝘃𝗶𝗱𝗲𝗿s' irinsu 𝗬𝗮𝗵𝗼𝗼, 𝗢𝘂𝘁𝗹𝗼𝗼𝗸, 𝗔𝗢𝗟, 𝗬𝗮𝗻𝗱𝗲𝘅, 𝗚𝗠𝗫 da sauransu. '𝗚' ta Gmail, na nufin '𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲', ma'ana '𝗲𝗺𝗮𝗶𝗹 𝗽𝗿𝗼𝘃𝗶𝗱𝗲𝗿' na kamfanin Google.
𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹 kamar layin waya ne (𝗧𝗦𝗣𝘀), shi kuma 'email' kamar Network Access Point (NAP) ne. Anan za mu iya kwatanta '𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹' da 𝗠𝗧𝗡, 𝗔𝗶𝗿𝘁𝗲𝗹, 𝟵𝗺𝗼𝗯𝗶𝗹𝗲 da 𝗚𝗹𝗼 a tsaran 'service 'providers'.
𝗬𝗮𝗵𝗼𝗼 𝗺𝗮𝗶𝗹, 𝗢𝘂𝘁𝗹𝗼𝗼𝗸 (𝗵𝗼𝘁𝗺𝗮𝗶𝗹 na 𝗠𝗶𝗰𝗿𝗼𝘀𝗼𝗳𝘁), da 𝗬𝗮𝗻𝗱𝗲𝘅 duk ɗaya suke da 𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹, duk 'email providers ne', kamfani ne kawai ya bambanta su, kamar yadda 𝗠𝗧𝗡, 𝗔𝗶𝗿𝘁𝗲𝗹, 𝟵𝗺𝗼𝗯𝗶𝗹𝗲 da 𝗚𝗹𝗼 suke a matsayin layikun gidan waya da zaka iya yin ƙira da su, aika saƙo ko siyan data, 'service provider' ne ya bambanta su.
Duk da muna da sauran '𝗲𝗺𝗮𝗶𝗹 𝗽𝗿𝗼𝘃𝗶𝗱𝗲𝗿' irin su
𝗬𝗮𝗵𝗼𝗼 𝗺𝗮𝗶𝗹,𝗵𝗼𝘁𝗺𝗮𝗶𝗹... amma 𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹 ya fi su amfanu musamman ga masu wayoyin Android. Zamu tattauna kan alfanin email a takaice a rubutu na gaba, kasancewar amfaninsa ba iya tura mail ba ne kawai.
Allah Ya datar da mu.
✍️ 𝗔𝗹𝗶𝘆𝘂 𝗠. 𝗔𝗵𝗺𝗮𝗱
20th Dhul-Qaadah, 1443AH
20th June, 2022CE
#AliyuMAhmad #FasaharZamani #SmartPhone #Hausa #Mail
0 Comments