Saboda tunawa da RANAR MAHAIFA, kar ka taiƙaita kewa ko nuna soyayya ko addu'ar alkhairi ga mahaifinka a iya ɗora hotunansa a SOCIAL MEDIA, don da yawa ba sa Social Media, wasu kuma Allah Ya musu rasuwa (Allah Ya jiƙansu).
Zai fi alkhairi ka masa biyayya a zahiri, ka tallafa masa a zahiri (daga-kai-sai-shi), ka masa addu'a a sirri, in kuna takun-saƙa ka je ku shirya, ka nemi albarkarsa da addu'o'in alkhairi cikin lamuranka.
Idan ya rasu, ka sadar da zumuncinsa (ga ƴan'uwansa da abokan arziki), ka ziyarci makwancinsa, ka masa addu'ar Allah Ya kyauta makwancinsa, ka gyara ɗabi'unka ta yadda in an ganka za a riƙa tuna alherinsa. Kar ka ci amanarsa wajen aikata abubuwan da ya haneka tun kafin kwanciyarsa.
KULLUM FATHER'S DAY ce! Iyayenmu sun cancanci ƙololuwar soyayya, kyautata da biyayya. Allah Ya ƙarawa iyayenmu albarka da lafiya. Waɗanda suka rasu Allah Ya kyauta makwancinsu ya albarkaci zuri'arsu, amin.
(c) Aliyu M. Ahmad
29th Shawwal, 1441AH
21st June, 2020CE
#AliyuMAhmad #FathersDay
0 Comments