MU GYARA HALINMU


Ko da an canja shugabanni, idan ba mu canja halayenmu ba, babu abin da zai canja.

Talaka shi yake neman hanyar da zai cuci dan uwansa talaka... ka dubi mai faci, lebura, burkila, 'yan barema, 'yan kasuwa... kowannensu zaka yi mu'mala da su sai an ce ma, ka yi hankali da mutane.

Yanzu kwanaki nake lura, idan iska tayar babur ta yi kasa, zaka yi zaton faci ne ko? Ka dauka ka je wajen mai faci, zai duba ya ga ko da kofar faci, in babu kofa wasu (masu facin) allura suke sawa su huda ma tif (su bata ma tif, ka kuma biya kudin faci)... talaka ne ya cuci talaka.

In burkila ko dan barema ka dauka aiki, bayan ba su je a kan lokaci ba, wasu sai su sace ma kayan aiki.

Idan ka dawo wajen 'yan kasuwa, kwata-kwata ba tausayi, ga tauye mudu, da dora muguwar riba. Wani dan kasuwar zai siya da araha, amma in ya zo siyarwa babu rangwame.

A tsakaninmu talakawan, babu tunani taimakekkeniyya, sai tunanin, ya zam sami wani abu a jikin dan uwana talaka... talaka ne yake cutar dan uwansa talaka.

A SIYASA

* Uwa-uba, talaka ne zai bi abin duniya, ya siyar da kuri'arsa, ya zabi azzalumai, su shugabance shi, ya dawo yana zaginsu... ana bawa mutane irinmu jagoranci, domin su jagorance mu da irin halinmu.

Talaka ne za a bawa wani hakki na tallafi ga dan uwansa talaka, ya cinye tun kafin abin ya zo gare shi...

إن الله لا يغير ما بقوم حتى يغيروا ما بأنفسهم

LALLE NE ALLAH BA YA CANJA ABIN DA YAKE GA, MUTANE SAI SUN CANJA ABIN DA YAKE GA ZUKATANSU. [Ra'ad, aya ta 11].

Allah Ya yaye mana damuwa, kunci da talauci.
Allah Ya gyara ma halayenmu.
Allah Ya zaba shugabanni nagari.

✍️ Aliyu M. Ahmad 
11th Dhul-Qaadah, 1443AH
11th June, 2022CE

Post a Comment

0 Comments