A tsawon kwanaki 114 da aka shafe ana yajin aiki...
1. Inda a kowacce rana, ana ma karatu na shafi guda (1) na Alkur'ani Maigirma, da a yau kana da shafi 114, (dai da hizfi goma sha-daya da rabi (11½) na Alkur'ani).
2. Inda kana fita neman kudi, a kullum kana asusun/ajiye ₦500 ko ₦1k, da a yau kana da ₦57k ko ₦114k ko fiye, naka ne halak mallak.
3. Inda kana zuwa koyon wata sana'a, dinki (tailoring), carpentry, welding, mechanic, hardware maintenance... da sauransu, cikin kwanaki 114 da tuni ka koya, ka ma fara cin moriyar kwarewarka.
4. Idan a cikin kwanaki 114 nan, kana zuwa majilissin karatu ko kina zuwa wata Islamiyya, da tuni wasu kananan littafan Fiqhu (irinsu Akhadary, Ishmawy...), da Ahadisul Ahkam (irin su Bulugh da Umdah) ka/kin kammala su, ko kuma ka/kin yi nisa a cikinsu.
Manzo ﷺ yana cewa: “akwai ni’imomi guda biyu (2) wadanda da yawan mutane suna tozarta su (ba sa amfani da su, sai babu su kuma mutum yana nadama), sune ni’imar LAFIYA da LOKACI (Bukhari, 6049).
Mu lura! Lokaci abu ne mai matuƙar muhimmanci da tsada a rayuwar ‘yan Adam da ba’a iya siyan sa da kuɗi. A kowacce rana ana bawa duk ɗan Adam awanni 24 (daƙiƙa 1440/ 86400 secs). Kuma in 1sec ya wuce ya tafi ba zai dawo ba. A matsayinka na Musulmi mai Imani, kana da sanin cewa, kowacce daƙiƙa sai an tambaye yadda ka tafiyar da ita a Alƙiyama.
Yanzu ma na mu makara ba, akwai asara babba, kana matashi, ka bata kwanaki 114 a gida, ba tare da ci ribarsu ba, a duniyance da a lahirance. Lalle akwai asara!
✍️Aliyu M. Ahmad
7th Dhul-Qaadah, 1443AH
7th June, 2022CE
0 Comments