YA ALAKARKA DA ALKUR'ANI?


Tsakaninka da Allah yaushe rabonka da ka bude Alkur'ani ka karanta?


إذا رأيت غبارا على مصحفك ؛ فاعلم أن الغبار على قلبك أشد


Idan ka ga kura (dust) akan Alkur'aninka, ka sani kura (da dattin) dake zuciyarka ya fi wannan yawa.


Daga tashinka a safiyar yau, zuwa yanzu mintuna nawa ka bata a social media? 10mins, 30mins, 1hrs... amma ka san a cikin mintuna 15 zuwa 25/30 zaka iya karanta cikakken izu daya?


Kai! Ko baka iya samun damar bude Alkur'ani saboda aiki ko wani uzurin, ka rika kunnawa (playing) kana sauraron sautinsa a lokacin aiki (idan babu hayaniya), daga sautikan Qurra' masu dadin murya; irin su Abu Bakr Al-Shatri, Ghamidy, Minshawy, Wahab Jibril, Minshary Al'afasy, Said Alkatib, Maher Al-Mueaqly, Al-Emady, Islam Sobhi, Yasser Al-Zailay, Mossad, Tareeq Muhammad, Kurdi, Al-Luhaidan...


Duk ranar da ta shude baka karanta Alkur'ani ko sauraronsa ba, ka yi babbar asararta, domin karanta Alkur'ani tamkar yin hira ne da Ubangiji (SWT). Na ga wasu har korafi suke masoyansu ko abokansu sun dau lokaci ba su 'chatting' ba, ina kuma kai da Ubangijinka?


اقرأ اخي، ورتل القرآن

اصدح بصوتك أسمع الأكوانا

اقرأ كلام الله داو نفوسنا

لنحس في اعماقنا، اعماقنا الايمانا

- بوخاطر


✍️ Aliyu M. Ahmad

6th Sha'aban, 1443AH

10th March, 2021CE

Post a Comment

0 Comments