Azkar na safiya da maraice yana da matuƙar tasiri ga lafiyar kwakwalwa, nutsuwa, tarin lada da samun tsarin Allah cikin/tsawon wuni.
Kana da isasshen lokaci! Ka ware mintuna 15 - 30 don ciyar ruhinka da Zikiri, kamar yadda kake ware lokuta don ciyar da gangar jikinka 'abin ci' daga bayan Sallar Asubahi har zuwa lokacin da rana zata fara dumi, Sallar Walaha (Dhuha). Da yammaci kuma, daga bayan sallar La'asar, har izuwa faduwar rana (Magriba).
Kuma dama tuni akwai samfur na irin Awrad da ya kamata ka lazimci yi tabbatattu daga Sunnar Ma'aiki ﷺ. Mafi sauƙi: Ayatul Kursi x1, Mu'awwidhatani x3, Salatin Annabi ﷺ x10, Hasbunallahu wa ni'imal wakil x7, Istigfari x100, Hailala x100, Subhanallahi wa bihamdihi x100... ku duba sauran cikin Hisnul Muslim da sauran littafan zikiri ingantattu.
Akwai asara sosai ka wuni baka yi wani abu na ambaton Allah ko yiwa Annabi ﷺ Salati ba. Allah Ya iya mana, Allah Ya karɓa mana, Ya ba mu kariya da kariyarSa, amin 🙏
✍️ Aliyu M. Ahmad
6th Jumada II, 1443AH
23rd December, 2020CE
0 Comments