#RamadanBasket
Ba laifi ba ne, in Allah ya baka hali ka kyautata; amma kafin ka burge budurwa, ka fara burge mahaifanka a gida.
Bal! Kyautatawa daya ce daga cikin shika-shikan soyayya. Soyayya sai da kyautatawa.
Ka iya bawa (wata) BUDURWA(r) kyautar ₦50k (wata) ta iya rainawa, wata ma ta bika da sunan wulaƙanci a bayan idonka (ɗan wahala/matsiyaci).
Amma inka bawa MAHAIFIYARKA kyautar ₦5k yini zata yi tana yima albarka da addu'a... zaɓi ya rage ga mai shiga rijiya.
(c) Aliyu M. Ahmad
13th Sha'aban, 1443AH
16th March, 2022CE
0 Comments