Duk talaucinka, jinyarka, duk mummunan halinka, kai ko mahaukaci ne kai iyayenka ba za su taba boyewa duniya kai dansu ba ne.
Amma me yasa (wasu) 'ya'yan yau ke boyewa duniya iyayensu saboda talauci, jinya ko (wata) kaddarar rayuwa?
Ya salam! Wallahi kar ka rudu da yawan ibadarka, ko yabo na kirki daga mutanen waje; wallahi ko limamin harami ne kai, in kana da matsala da iyayenka, ka yi kokarin ku daidaita.
Don ba zaka shiga aljanna ba sai ka sami yardar Allah. Ba zaka sami yardar Allah ba, har sai iyayenka sun yarda da kai.
(c) Aliyu M. Ahmad
15th Sha'aban, 1443AH
18th March, 2023CE
0 Comments