Kwaret: Somin Tabi

#Kwamaret: Somin tabi!



Tun a shekarar 2011 na dauki al'adar rubuta muhimman abubuwa da suke faru a rayuwata, wato diary (a Turance). Zai wuya na manta mutum, ko wata mu'amala da muka yi da shi, mai dadi ko maras dadi. Kai! Ko na manta, tana nan a tubuce a cikin 'diary'. Zan iya hakaito ma mu'amalarmu da kai, tare da rana, wuri ko lokaci in na bude 'diary'.


Ba babin kwamaranci, wannan labarin babba ne, ina bude 'diary' na gan shi da 'jan rubutu' 🤔


Ya Ameer! Yusuf Garba Muhammad, Allah Ya gafarta mana. Zaka iya tuna ranar Juma'a 7th ga watan Janairu, 2022 Miladiyya? Astagfirullah, Allah na tuba! Tun da nake a rayuwata, a ce ina gari, ba a halin tafiya ko jinya ba, ban taba hada sallah 3 a lokaci daya ba sai a hidimar kwamaret. Su kuwa su Ameera da Deputy Ameera Ummu Sheikhil Islam, 'yan matan nan; guduwa suka yi suka je sauke farali.


Kuma abin mamakin ma, wai a kwamaranci addini, Muslim Students Society (MSSN), balle na Aluta, balle na asalin gwagwarmaya ✊. La'asar, Magriba da Isha'i 🥺 a waje guda 😢ban mancewa da wannan, daidai gwargwadon iyawa, muna addu'a Allah ya bamu ikon tsadai farali akan lokaci.


Ba wai ina tona mana asiri ba ne, a'a nasiha zan mana kwamarawa, komai rintsi, komai hidima, a rika kokarin yin sallah a kan lokaci. Allah ya sakawa (H)abibty da alheri. Ta ce, "Allah Yaya kar sake irin wannan, ai Sallah gaba take da komai." 


Kwamaranci yana da alheri, yana kuma da sharri, daga cikin sharrukansa akwai jinkirta sallah in ana hidima. Allah Ya bamu ikon kiyayewa 🙏 7th January, I dey still remember, bana fatan na sake maimatawa. 


(c) Aliyu M. Ahmad

15th Sha'aban, 1443AH

18th March, 2022CE

Post a Comment

0 Comments