AREWA24: KWANA CASA'IN

 #AREWA24 #KwanaCasain



Ba lalle yadda na lissafa ya zama daya naka ra'ayin ba, ra’ayina ne. 


Arewa24 sun ce, za su fara haska shirin KWANA CASA’IN zango na 7 (session 7) rana Lahadi, 3 ga wanan Afrilu , 2022.


Ranar da za su fara haska shirin nan, ana sa ran ta kasance 2 ga watan Ramadhan na 1443 Hijiriyya. 


Sannan lokacin (8:00 na dare) zai yi daidai da lokacin da yawancin Masallantanmu ke gabatar da ibadar Sallar Asham (Taraweeh).


Ramadhan yana da kwanaki 29 ko 30 ne. Ina ga dudu shirin nan sau 4 ko 5 za a haska shi gaba daya a watan Ramadhan, (ba wai kullum da kullum ba) a ranakun Lahadi na kowanne sati:


3rd April, 2022 (2 ga Ramadhan)

10th April, 2022 (9 ga Ramadhan)

17th April, 2022 (16 ga Ramadhan)

24th April, 2022 (23 ga Ramadhan)

24th April, 2022 (23 ga Ramadhan)

1st May, 2022 (30 ga Ramadhan ko ranar Sallah) 


Gaskiyar magana, in mutum na da niyyar Ibada, bana tsammani kallo zai hana shi. 


In ma kana da niyyar kallon ma, sallah ba zata hanaka ba. Tunda suna dorawa a Youtube Channel nasu, ka iya zuwa ka sauke daga baya. To wai ma dole ne kallo? 


In sun haska, kar ka tsaya kalla, kuma ka hana iyalanka kalla, faqat!


Laifinmu ya fi yawa ai! Da yawa suna zaginsu a fili, amma ka duba wayoyinsu, ko me iyalansu ke kalla a gidajensu? 


Mu muke 'promoting' dinsu. Yadda muke rawar kafa kallo shirye-shiryensu muna yiwa tashoshin yada addini?


© Aliyu M. Ahmad

Juma'a 28th Sha'aban, 1443AH

25th March, 2022CE.

Post a Comment

0 Comments