GHAYRAH - Ni kam ina kishinta...

 


 


Za ku je daurin aurena dai, amma ba zan yarda ku kalla min mata ba; wajena kuka je, ba wajen Madam ba; balle har wani kato, kamata; ya rabeta, ya yi hoto da wacce aka daura mana aure... ya dora a media da nufin taya ni murna.

 

Ka dai iya yada hotona, amma ban da na Madam; cab! matar tawa na ga hotonta na yawo a media! Sam!


Matata suturata ce, ni kadai aka aurawa, ban jin zuciyata zata aminta na nunawa duniya kyawunta da kwaliyyarta... tab! Allah ya sawwaka kunnena ya ji wani yana ambata lr kyawun surarta ️🤜

 

Matata ta gaban farin cikin gidana ce, tarbiyar 'ya'yana, ba ta gaban sakawa a gaban mota ba. Kai! Ni kam bani da rashin kishin da Madam zata fito bainar al'umma tana jujjuyawa tana rawa, har wani kato yana siffanta surar jikinta.

 

A kan kishi, Bukhari ya ruwaito a hadisi na 6980 cikin Sahih nasa, daga Mughira, Sa‘d ibn ‘Ubaadah (RA) ya ce: "ة لو رأيت رجلا مع امرأتي لضربته بالسيف غير مصفح فقا" Ma'ana: "Da zan ga wani tare da matata, da sai na sare shi da takobi". Sai Manzon Allah ya ce: "Shin kuna mamakin kishin Sa'adu ne? Lallai ne ni, na fi shi kishi! Kuma Allah Ya fini kishi".

 

A cikin Alkur'ani Maigirma; Allah ya umarci Annabi da cewa: "يا أيها النبي قل لأزواجك وبناتك ونساء المؤمنين يدنين عليهن من جلابيبهن ذلك أدنى أن يعرفن فلا يؤذين..." Ma'ana: "Ya kai wannan Annabi, ka cewa matanka, da ‘ya’yanka da mata muminai da su janyo tufafinsu ya rufe jikin su gaba daya…” [Ahzab; aya ta 59]. A cikin Musnad Ahmad, hadisi na 5372; Manzon Allah ya ce: "Duk wanda ba ya kishin iyalinsa, ba zai shiga Aljannah ba".

 

Wato zamani ya zo, da sunan wayewa; babu kishi sam irin yadda ake gudanar da bukukuwan aure. Matarka da aka daura muku auren Sunnah, ta fito gaban karti tana tika rawa da sunan wayewa; karti na likewa a jikinta suna hoto da lika mata kudi... Ba da Aliyu ba wannan wayewar kam; don ni ina matukar kishinki my future wife 😘 daga ni sai ke 🥰

 

(c) Aliyu M. Ahmad

20th J/Awwal, 1443AH

25th December, 2021CE

Post a Comment

1 Comments