Ita fa ranar tunawa da Harshen Hausa, ba an ƙirƙire ta don yaɗa karin magana kaɗai (only) ba ne, a'a; dama akan ware wasu kwanaki ne don tunawa da abubuwa masu muhimmanci ga al’umma da rayuwarsu, don zaƙuluwa da kuma nazari wasu ƙalubale da koma-baya da ke tattare da wannan abu (misali Harshe, Hausa), tare da tattauna yadda za a shawo kan waɗannan ƙalubale. Ko kuma nazari kan ci gaba da wannan abu ya samu.
Misali, za mu iya tattaunawa a kan wasu ƙalubale da ke fuskantar Harshen Hausa da Hauwasa kamar haka:
• A wane yanayi Harshen namu na Hausa yake a yanzu? Wane ƙalubale yake fuskanta?
• A wane hali rayuwar Hausawa da al'adunsu ke ciki a wannan ƙarni? Wane ƙalubale ke fuskantarsu?
• Shin Harshen Hausa da al'ummar Hausawa suna tafiya da zamani (Ƙarni na 21) ta fuskar ƙirƙire-ƙirƙire (innovation), fasaha (technology) da kimiyya (science)?
• Shin kun san cewa, mafi yawa cikin Hausawa da ke amfani da kafar sadawar zamani (Social Media) suna rubutu da Harshen Hausa amma cike da kura-kuran Nahwun Hausa? Mene ne sila da kuma hanyoyin rage wannan matsalar?
• Me yasa kashe-kashen mutane da ake a ƙasar nan akan Hausawa yake ƙarewa?
• Shin mun sani cewa, akwai makarantun 'ya'yan Hausawa da aka soke koyo da koyar da Harshen Hausa cikin jadawalin karatu, ciki har da firamare da sikandire? Mene ne dalilin haka, kuma wane ƙalubale zai jawowa Harshen a gaba?
• Me yasa Hausawa dake karantar yaren Hausa a jami’o’i suke kyamar ko kunyar nuna kansu cewa suna karantar Hausa? Wayewa ne ko ci baya?
Da ma wasu kalubale da dama. Amma a nazarce, mun ci gaba a zamanance, adadinmu (population) na ƙaruwa, nazarin harshen na ƙaruwa a kasashen ketare (foreign countries), amma al’adunmu na tafiya, kuma Harshen na mutuwa a hannayenmu (wajen rubutu), kuma karance-karance cikin yaren ma na raguwa.
Yarena, abin alfaharina.
© Aliyu M. Ahmad
5th Dhul-Qadah, 1442AH
26th August, 2021
NB: Tsohon rubutu ne.
0 Comments