Azumtar watan
Ramadhana yana zama wajibi akan dukkan wanda WAJIBAN SHARUDDAN AZUMI suka
tabbata akansa kamar haka:
1. MUSULUNCI
Yana daga cikin
Sharuddan Wajibcin Azumin Watan Ramadhan; mutum ya kasance Musulmi wanda yayi
imani da Allah, Manzon Allah (S.A.W.) da kuma abin da Allah Ya aiko da Annabi (S.A.W.);
- Misali: Qur’an Nisa’i aya ta 136
Azumin watan
Ramadhan baya halatta akan kafiri, wa lau Ahlul-Kitabi (Yahudu da Nasara) ko
wanin su. Dalilin da ya sa na ce na Ramadhan kawai ga Musulmai shi ne; saboda
su ma wadanda suke sauran addinai musamma Ahlul-Kitabi (Yahudawa da Nasara) a
baya an wajabta musu Azumi k amar yadda Allah Ya fadi a cikin Alkur’ani (Qur’an;
Baqara aya ta 183) amma ba a irin lokacinmu ba (Watan Ramadhan) kuma har yanzu
wasunsu suna yin ibadar Azumi.
Misali:
Yahudu suna Azumin
Pilegesh Bagiva, Nadab & Abihu, Gadaliah, Tammmuz, Miriam, Yom Kippur Katan,
Tevet, Purim, Esther, Khmelnytsky. Nasara su Azumin Great Lent, Holy Week,
Nativity Fast, Apostle’s Fast & Dormition Fast) - Qur’an; Baqara aya ta
183; Bible: Isaiah, chapter 58:6-7, Zachariah, chapter 7:5-10, Daniel, 8-16; Torah:
2 King 25:25-26; The Three Weeks: Mouring the Destruction Torah.org
2. HANKALI
Hankali
sharadine daga cikin Sharudan Wajibcin Azumin Watan Ramadhan bayan kasancewar
Musulmi. Azumi baya halatta ga wanda hankalinsa ya gushe (mahaukaci), kamar
yadda aka ruwaito Hadisi daga Annabi (S.A.W.) hadisi Sayyadina Ali (R.A.):
"رفع القلم عن ثلاثة؛ عن النائم حتى
يستقظ، وعن الصبي حتي يشب، وعن المعتوه حتى يعقل"
“An dauke
alkalami (ba za’a rubuta aiyukan) akan mutane guda uku (3):1. Mai bacci har sai
ya farka (daga baccinsa); da 2. Yaro karami (wanda bai balagha ba) har ya tasa
(balagha); 3. Mai tabin hankali (Mahaukaci) har sai ya dawo cikin hayyacinsa
(hankalinsa)”
– Tirmidhi ne
ruwaito a hadisi na 1423; Ibn Majah, 2041; Nisa’i a cikin "الكبرى" 7346; Abu Dawud, 4397 / 4402 /
4403.
3. BALAGA
Azumi ya wabaja
akan wanda ya kai kimar Mukallafi (Balagha), Azumi bai wajaba akan yaro wanda
bai Balaga ba, kamar yadda yazo a Hadisin sama (Hadisin Sayyadina Ali ibn Abu
Talib [R.A.],Tirmidhi 1423).
Matakin Balagha
Balagha tana
tsakanin shekaru 10, 11 – 15 ga mace; shekara 14, 15 – 18 ga namiji kamar yadda
magabata da kuma masana fannin lafiya na zamani suka tauttauna akai (MishkatulMasabih juzu’i na 2 shafi na 724).
Sannan akwai alamomin
da suke nuna cewa mutum ya kai matsayin Mukallafi (balagagge), yawanci sun fi
tasiri akan abubuwan da suke fitowa na Zahiri kamar haka:
Ga mace:
Fara jinin al’ada,
fitowar mama (nonuwa) a kirji, budewar farji, fitowar gashi a hammata da kuma
gaba, warin jiki da kara kaurin jiki (Mitchell et al (2011). "Genetic basis and variable phenotypicexpression of Kallmann syndrome: towards a unifying theory.". Trends Endocrinol Metab. 22 (7) p. 250).
Ga namiji:
Fitar maniyyi a
farke ko a yayin bacci (mafarki); fitowar gashin hammata, fashewar murya, karin
girma mazakuta dss (Krueger H,
Osborn L. Effects of hygiene among the uncircumcised. J Fam Pract. 1986; 22 (4) :353–5).
Game da Azumin
Yara (Wadanda basu Balagha ba)
Ga me da azumin
yara (wadanda basu Balagha ba) an sami ruwaya ga Ibn Khuzaima wacce Rubayyibint Mu’awwiz (R) ta ce:
"...نصوم صبياننا، ونجعل لهم اللعبة من
العهن، فإذا بكى أحدهم على الطعام، أعطيناه ذاك حتي يكون عند الإفطار"
“…Muna Azumtar
da kananan yaranmu, kuma muna yi musu abin wasa na bugaggiyar auduga, idan
dayansu yayi kukan yunwa sai mu bas hi wancan abin wasa, har lokacin buda-baki
yayi”
A taikace da
yana da kyau idan yaro ya dan fara wayo (idan ya kai shekaru 10-13 da haihuwa);
ana barshi ko ana kwadaitar dashi yin Azumi domin ya saba kafin zuwan lokacinsa
na wajibi, kamar yadda ya gabata a sama.
4. LAFIYA
Bayan
kasancewar mutum Musulmi, mai hakali kuma ya kai matakin Balagha; to dole sai
ya kasance yana lafiya da dama ta yin Azumin tukun Azumi ke zama wajibi akan,
kamar yadda ya zo karara cikin Al-Qur’ani Mai Girma (cikin Suratul-Baqarah aya
ta 184), inda Allah (S.W.T.) Ya ke cewa:
…
وَمَن ڪَانَ مَرِيضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنۡ أَيَّامٍ
أُخَرَۗ
Fassara:
“…wanda daga
cikinku ya kasance cikin rashin lafiya ko halin tafiya sai ya rama (abin da bai
azumta ba) a wasu kwanaki…”
Ga wanda larurace
mai yankewa (mace mai ciki, haila, jinin biki) ko wanda rashin lafiyar tasa mai
warke wace sai ya rama in Allah ya bashi sauki (lafiya) kamar yadda ya zo cikin
ayar Suratul Baqara ta sama, idan kuma wanda mutum ya tsufa-tukuf ba halin yin Azum
ko mai jinya da kwararun likitoci sun tabbatar da cewa ba zai warke ba sai ya
ciyar da miskinai (Baqara aya ta 184). Allah ne mafi sani.
5. MAZAUNIN
GIDA
Ga wanda zai yi
tafiyar ta kai Mil Arba’in da Takwas (kimanin Kilometer 77) ya iya ajiye Azumi
ina yaso, in ya ga ba zai wahala ba ya iya dauka, kamar yadda Ayar Al-Qur’ani ta
nuna (Suratul-Baqarah aya ta 184), da kuma Hadisin Abu Sa’id al-Khudry cikin
Sahih Muslim sai yayi Azuminsa in ba takura.
أَيَّامًا مَّعۡدُودَٲتٍۚ
فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنۡ أَيَّامٍ أُخَرَۚ
وَعَلَى ٱلَّذِينَ يُطِيقُونَهُ ۥ فِدۡيَةٌ طَعَامُ مِسۡكِينٍۖ فَمَن تَطَوَّعَ خَيۡرًا
فَهُوَ خَيۡرٌ لَّهُ ۥۚ وَأَن تَصُومُواْ خَيۡرٌ لَّڪُمۡۖ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Fassara:
“Kwanuka kidayayyu. To, wanda ya kasance majinyaci (mara lafiya)
ko kuwa yana cikin halin tafiya sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam.
Kuma a kan wadanda suke yinsa da wahala akwai fansa; ciyar da miskinai, sai dai
wanda ya kara alheri, to, shi ne mafi alheri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da
wahalar) ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance kuna sani” – Baqara ayata 184
_________
To be
continued… in sha Allah.
19th Sha’aban,
1438 AH
(16th May, 2017
AD)
0 Comments