Rukunai jam’i ne ba kalma rukuni, ita kuma kalmar
rukuni ararriyar kalmace daga yaren Larabci wato rukunun (ركن);
ita kalmar ‘ركن’ tana nufin ‘kusurwa’ ko kuma ‘corner’ a Turance, ko ‘kaso’ ko
kuma ‘bangare’ ko ‘asasu’ (i.e. tushe) kamar yadda ابن منظور
mai littafin لسان العرب a shafi na 1721 yayi bayaninta a cikin
littafin; Hans Wehr shafi na 378; Al-Mawrid shafi na 594.
Saboda haka, anan kalmar RUKUNAI ko RUKUNAN AZUMI, ana nufin ginshikan turaku
na Ibadar Azumi.
Ibadar Azumin (ita
ma) tana da nata rukunai kamar yadda sauran ibadu suke da nasu. Rukunan Azumi guda uku (3) ne:
1. Niyya
2. Lokacin
kamewa
3. Kamewa daga
barin abin da ke bata azumi
Bayanin kowanne zai zo daga baya insha Allah. Niyya da ma’anarta,
sharadanta, yadda ake jaddata, muhallinta da kuma yadda take tabbata. Lokacin
kamewa, lokacin da yake farawa, bayanin kan Alfijir, farin zare baki da fari,
faduwar rana dss. Kamewa, ma’anarta da sharuddanta.
___________________
To be continued… in sha Allah
20th Sha’aban, 1438 AH
(17th May, 2017 CE)
0 Comments