GUZURIN RAMADAN VI: WAJIBCIN AZUMIN WATAN RAMADHAN




Azumin Ramadhan ya cikin jerin ibadu na asasun addinin Musulunci (أركانالإسلام); Azumin Ramadhan ya cikin jerin Azumunmuka da Sharia Musulunci ta wajabta shi a duk shekara a cikin watan (Ramadhan) ga dukkan wanda sharuddan azumi suka hau kansa; wajibi ya azumci watan Ramadhan 29 Ko 30.

Kamar yadda Allah (S.W.T.) ya fada cikin Al-Qur'ani Mai Girma Suratul Baqara aya ta 183;

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡڪُمُ ٱلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِڪُمۡ

Fassara:
"An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabtawa wadanda suka gabace ku…" – Baqara, aya ta 183

ۚفَمَن شَہِدَ مِنكُمُ ٱلشَّہۡرَ فَلۡيَصُمۡه

Fassara
"...duk wanda ya halarci watan daga cikinku (to) ya azumce shi…" – Baqara, aya ta 185

Yazo cikin Hadisin Bukhari No. 1891, Hadisin Talha bin Ubaidulla  (R.A.) wanda ya kawo kisar wani Balaraben Kauye da yake tambayar Annabi akan Ibada, da yake cewa:

"يا رسول الله... أخبرني بما فرض الله علي من الصيام؟ فقال: "شهر رمضان، إلا أن تطوع شيئا"

Fassara:
“Ya Manzon Allah!…Ka bani labarin abin da Allah Madaukakin Sarki ya farlanta a kaina na Azumi. Manzo Allah (S.A.W.) Ya ce (masa); Azumin watan Ramadan  (gaba dayansa), sai in ka so ka iya yin na Nafila” - Bukhari hadisi na 1891

A ruwayar gaba; wacce aka karbo daga Nana A’isha (R.A.) ita ma cikin Sahih al-Bukhari hadisi na 1893 ta ce:

أن قريشا كانت تصوم يوم عاشوراء في الجاهلية،  ثم أمر رسول الله صلى عليه وسلم بصيامه حتي فرض رمضان…

Fassara:
“Quraishawa sun kasance suna Azumtar ‘Ashura’ (10 ga watan Muharram) a lokacin Jahiliyya (kafin zuwan Annabi [S.A.W.] da sakon Allah); sai Manzon Allah Ya bada umarnin (ga Musulmai su ma) su na Azumta(r Ashura); har sai da aka farlanta Azumin Ramadha (Baqarah aya ta 183)…” - Sahih al-Bukhari hadisi na 1893

Ya na daga cikin hujjar wajabcin Azumin Watan Ramadhan hadisin Abdullahi dan Umar (R.A.) na shika-shikan Musulunci (أركان الإسلام) :

" بُنِيَ  الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ: شَهَادَةِ أَنْ لَا إلَهَ إلَّا اللَّهُ  وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ  الزَّكَاةِ، وَحَجِّ الْبَيْتِ، وَصَوْمِ رَمَضَانَ".
An gina Musulunci a bisa abubuwa guda biyar;  1. Shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, (kuma) Annabi Muhammad Manzon Allah ne; 2. Tsaida Sallah; 3. Bayarda Zakkah; 4. Ziyartar Dakin Allah Mai alfarma (Aikin Hajji); 5. AZUMTAR WATAN RAMADANA” - Bukhari (8, 4515); - Muslim (16); Tirmidhi (2609); Nasa’i (5001), Ibn Majah (158, 1336).

A takaice Azumtar watan Ramadana daya ne daga cikin rukunan Musulunci; kuma wajibine yinsa kamar yadda gaba dayan Musulmai suka yarda; tun daga kan Sahabbai, Tabi’i…har zuwa yau walau Sunni, Shi’a, Qur’aniyyun (Baqara; 183) dss; kuma duk wanda yaki ko kin yarda da wajibcin hakika ya juyawa Alkur’ani; Maganar Allah da kuma Sunnar Manzon Allah (S.W.A.) baya;  Qur’an: Taha, 123-124; Ali’imran, 31; Aaraf, 157; Nisa’i, 59, 170; Juma’a, 2. Majma’uz-Zawa’id 1/47; Fiqhus-Sunnah 1/433; Alkaba’ir (Dar El Fikr) p. 27; أحكام ومسائل رمضانية: المنجد p. 13;  محمد إبن جمل :أركان الإسلام والإيمان وما يجب أن يعرفة كل مسلم عن دينه p. 177(.


_________
To be continued… in sha Allah.


18th Shaaban, 1438 AH
(15th May, 2017 AD)


Post a Comment

0 Comments