GUZURIN RAMADAN IV: MA’ANAR AZUMI (SAWM)


MA’ANAR AZUMI (SAWM)


Azumi fassara Kalmar Larabci ne na "الصوم" Sawm’.

Ita kuma kalmar "الصوم"  a yare "لغة" tana nufin "الإمساك"  ma’ana ‘kamewa’ ko ‘bari’ (Hans Wehr p. 550)

Amma a Shar’ance azumi shi ne kamar yadda أبوبكر جابر تالجزائر ya ke fadi a cikin littafinsa منهاج المسلم  shafi na 247 bugun gidan مكتب العلوم والحكم na gidan الدار السلام shafi na 232 yace:

الصوم: الإمساك عن الأكل والشرب وغشيات النساء، وسائر المفطرات من طلوع الفجر إلى غروب الشمس

Ma’ana:
Azumi shi ne kamewa daga ci, da sha, ga kauracewa mata da sauran kayan ciye-ciye tun daga fitowar rana har izuwa faduwarta.

ابنمنظور mai littafin لسان العرب  a shafi na 2529 kuma cewa yayi:

الصوم: ترك الطعام والشراب والنكاح والكلام

Ma’ana:
Azumi shi ne barin abinci, da abin sha, da aure da zance.

Anan shi [ابن منظور] ya kara da ‘barin zance’, amma yance da ba shi da amfani ake nufi, Allah Shi ne Mafi sani).

Saboda haka, idan muka lura a Shari’ance idan ance azumi shine:
Barin cin abinci, da shan abinsha, da kauracewa mata (a lokacin azumi) da barin yarfaffun zantuka  (zance marar amfani) tun daga fitowar alfijir har izuwa faduwa rana, kamar Allah (S.W.T.) Ya fadi a cikin Alkur’ani Maigirma:


GABOBIN MA’ANONIN AZUMI DAGA ALKUR’ANI MAI GIRMA:

1. Kamewa daga Ci da Sha daga Alfijir zuwa Faduwa Rana:

وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَيۡطُ ٱلۡأَبۡيَضُ مِنَ ٱلۡخَيۡطِ ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِۖ ثُمَّ أَتِمُّواْ ٱلصِّيَامَ إِلَى ٱلَّيۡلِۚ

Fassara:
“…ku ci kuma ku sha har silili fari ya bayyana a gare ku daga silili baki daga alfijiri. Sa’an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare…” - Suratul Baqarah aya ta 187

2. Kauracewa mata (jima’i) lokacin azumi (tun daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana); fadin Allah (S.W.T.) a aya ta 187 ta cikin Suratul Baqara:

أُحِلَّ لَڪُمۡ لَيۡلَةَ ٱلصِّيَامِ ٱلرَّفَثُ إِلَىٰ نِسَآٮِٕكُمۡۚ هُنَّ لِبَاسٌ لَّكُمۡ وَأَنتُمۡ لِبَاسٌ لَّهُنَّۗ

Fassara:
“Saboda haka an halarta a gare ku, a daren azumi, yin jima’i (saduwa) da matanku, su tufa ne a gare ku, kuma ku tufa ne a gare su…” - Suratul Baqarah aya ta 187


3. Kamewa harshe (barin yawaita zance):

إِنِّى نَذَرۡتُ لِلرَّحۡمَـٰنِ صَوۡمًا فَلَنۡ أُڪَلِّمَ ٱلۡيَوۡمَ إِنسِيًّا

Fassara:
“…Lallai ne, na yi alwashin azumi domin Mai rahama, saboda haka ba zan yi wa wani mutum magana ba”  - Suratul Maryam, aya ta 26



_________
To be continued… in sha Allah.


Aliyu M. Ahmad
16th Shaaban, 1438 AH
(13th May, 2017 AD)

Post a Comment

0 Comments