CamelCase 🐪🐫


CamelCase 🐫🐪

Salon rubuta kalma ne a kalma mai ɗauke da kalmomi guda biyu da suke a haɗe (closed compounded words), a inda kalma ta biyu za a rubuta ta da babban baƙi (uppercase/capital letter).

A wannan salon, kalmar ta kan iya kasance, harafin farko babba (uppercase, kamar a SalFat) ne ko ƙarami (lowercase, kamar a 'iPhone'), kawai dai a kalma ta biyu za a rubuta ta da babban baƙi (majuscule) kamar yadda yake a tozon bayan rakumi 🐪🐫 (hump). 

Idan ya fara da babban baƙi, kuma harafi na biyu ma babba ne, ana ce masa 'Pascal Camel Case', kamar a SalFat na sama. Idan kuma da ƙaramin harafi ya fara, na tsakiya kuma babba, 'camelCase'.

Misali:

Whats + App = WhatsApp ne ✅, ba Whatsapp ba ❌. Kula! 'A' ta tsakiya ana rubuta ta da babban baƙi ne (camelCase).

WhatsApp ✅
Whatsapp ❌

CapCut ✅
Capcut ❌

YouTube ✅
Youtube ❌

TikTok ✅
Tiktok ❌

JavaScript ✅
Javascript ❌

ChatGTP ✅
Chatgtp ❌
ChatGtp ❌

iPhone ✅
iphone ❌
Iphone ❌

LikedIn ✅
Likedin ❌

PowerPoint ✅
Powerpoint ❌

WordPress ✅
Wordpress ❌

PlayStation ✅
Playstation ❌

PayPal ✅
Paypal ❌

MasterCard ✅
Mastercard ✅ shi ana iya rubutawa da duk salo biyun.

AliExpress ✅
Aliexpress ❌

CamScanner ✅
Camscanner ❌

OneDrive ✅
Onedrive ❌

PalmPay ✅
Palmpay ❌

PixelLab ✅
Pixellab ❌

QuillBot ✅
Quillbot ❌

Ga SalFat ✅ na Salisu Saheel, ba Salfat ❌ ba.

ResearchGate ✅
Researchgate ❌

VidMate ✅
Vidmate ❌

Yana daga cikin ƙa'idojin rubuta irin waɗannan kalmomi da ya kamata a kiyaye a rubuce-rubuce, musamman a rubuce-rubucen ilimi.

Sannan kuma camelCase, wani lokacin akan ƙira wannan salon da 'internal capitalization', ko 'camelCaps', ko 'medial capitals', ko 'pascal case', 'wikiWord/wikiCase', 'dromedary' da sauransu.

✍🏻Aliyu M. Ahmad
4th Dhul-Qidah, 1445AH
13th May, 2024CE

#AliyuMAhmad #AliMotives #RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments