GUZURIN RAMADAN I - MA'ANAR RAMADHAN



MA'ANAR RAMADHAN

Ramadan: Kallamar Labaranci ce wacce aka ciro ko juyota (derived) daga Kalmar (RAMIDHA) "رمض"  - ‘AR-RAMADHU’ ko ‘AR-RAMDHA’U’.' Shi kuma Kalmar رمض"tana nufin; tsananin zafi "شدة الحر" kamar yadda ya zo a Hans Wehr p. 379, Lisal al-Arab p. 1729 da kuma Almawrid p. 595. Kamar yadda Larabawa suke cewa:

استجار من الرمضاء بالنار

RAMADHAN shi ne wata na tara (9th) a jerin watannin goma-sha-biyu (Qur’an: Tawba: 36) na shekarar/kalandar (calendar) Musulunci. Watan Ramadhan shi ne watan da Musulmai ke yin ibadar Azumi (daya daga cikin rukunan Musulunci; Bukhari, 8), kamar yadda ya zo a cikin Alkur’ani Suratul Baqarah aya ta 185.

An sayawa watan Ramadhan sunansa (RAMADHAN) saboda watane da yake zuwa a yayin da ake tsananin zafin rana (kamar yanayi [wheather] da muke ciki a yanzu har zuwa Ramadhan), sannan a cikinsa ake kone zunubin masu imani.

Abu Abdullah Muhammad ibn Ahmad ibn Abu Bakr al-Ansari al-Qurtubi, a cikin Tafseer al-Qurtubi 2/271-2:

“(Idan muka duba) Watan Ramadhan yana tattare da tsananin zafin rana, da kuna da kishirwa… Labarawa suke fadin wannan kalmar (wato 'ar-RAMD' wacce ake kiran watan 9 RAMADHAN da 'RAMADAN') to za mu ga cewa ya zo daidai da lokacin da yake akwai tsananin zafin rana... An sanya masa wannan sunan domin yana kone zunubai…”.

Sannan Kalmar RAMADHAN ta zo cikin Al-Qur'ani Mai Girma karara sau daya ne, wadda aka ambata cikin Suratul Baqarah aya ta 185; wato:

شَہۡرُ رَمَضَانَ ٱلَّذِىٓ أُنزِلَ فِيهِ ٱلۡقُرۡءَانُ هُدًى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَـٰتٍ مِّنَ ٱلۡهُدَىٰ وَٱلۡفُرۡقَانِۚ فَمَن شَہِدَ مِنكُمُ ٱلشَّہۡرَ فَلۡيَصُمۡهُۖ وَمَن ڪَانَ مَرِيضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنۡ أَيَّامٍ أُخَرَۗ يُرِيدُ ٱللَّهُ بِڪُمُ ٱلۡيُسۡرَ وَلَا يُرِيدُ بِڪُمُ ٱلۡعُسۡرَ وَلِتُڪۡمِلُواْ ٱلۡعِدَّةَ وَلِتُڪَبِّرُواْ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَٮٰكُمۡ وَلَعَلَّڪُمۡ تَشۡكُرُونَ ۝

"Watan Ramadan ne aka saukar da Al-Qur'ani..."

_______
To be continued… in sha Allah.

15th Shaaban, 1438 AH
(10th May, 2017 AD)

Post a Comment

0 Comments