Idan yau kana aiki, ana ba ka ₦5k a wata, matuƙa ₦5k tana biya maka buƙata, ka riƙi aikinka abinka MATUƘAR BA KA SAMI WANDA YA FI SHI BA.
Wanda yake ganin wahala kake, ya ba ka wanda ya fi shi mana. Kada ka biyewa 'YAN SOCIAL MEDIA da MAGANAR MUTANE. Za su kashe maka gwuiwa kan wanda ka samu, ba kuma za su samar maka wanda ya fi shi ba, wanda su suke tsammata maka.
Ko kana da burin yin wani aiki ko sana'a ba ka samu ba, to ka riƙi wani (da ya zo maka a yanzu) kafin wanda ke mafarki ya zo, ka kuma ci gaba da lalumen hanyoyin da za ka kai ga 'dream job' naka. Kanka kake yi wa rayuwa ba kowa ba, sai dai idan don burge mutane kake rayuwa kuma, to!
₦50k da kake ganin ta ba a bakin komai ba, wani ita yake nema ido rufe, kamar yadda ₦1 million take kuɗi a wajenka, ba ta fi ƙarfin wani ya yi maka kyautarta yanzu-yanzu ba. Mu riƙa bambance tsakanin MOTIVATION, da kuma ɗorawa mutane PRESSURE, son daidaita rayuwarmu da wasu (na ƙasa da mu). Mu ma a wajen wasu ba koman-komai ba ne, idan aka auna ta fuska samun 'incomes'.
Kamar shekara 5 baya, akwai labarin wani yaron Alhaji da Alhaji ke biya ₦10k a duk wata, amma kuma a shagon zai yi breakfast, ya ci abincin rana (launch). Idan an tashi a shago za a ba shi ₦300 kuɗin transport kullum. Sai wani abokinsa ya zuga shi, wai ₦10k ta yi kaɗan, nawa suke nemawa Alhaji riba a kullum?
Yaron Alhaji ya fara wasu ɗabi'u, har Alhaji ya yi masa magana, lafiya kuwa? Sai ya ce, shi gaskiya ₦10k ta yi masa kaɗan a wata, ko dai a ƙara masa, ko kuma ya ajiye aiki. Alhaji ya ce, ba abin da zai iya ƙara masa. Sai ya ajiye aiki, ya tafi.
Ya fi shekara 2 ba aikin yi, ga shi bai iya sana'ar hannu ta komai ba. Hatta abincin da zai ci ya fara gagarar sa, ya dawo wajen Alhaji, Alhaji ya ce, ya samu madadinsa, ya yi haƙuri.
Abin da yake wahalar da mu, RASHIN SANIN KAI (self-awareness). Idan ba ka san kanka ba, za ka yi ta kwatanta kanka da wasu, ka manta da ni'imar da Ubangiji ﷻ ya yi maka, ko kuma kana raina mutane da ƙasƙantar da su saboda kana ga ka fi su (kamar wayonka ne ya ɗauka ka sama da su).
✍️ Aliyu M. Ahmad
8th Sha'aban, 1446 AH
6th February, 2025 CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments