Idan Kana Cikin Fushi!

Idan kana cikin fushi!

Kar ka yi furuci alhalin kana cikin fushi, domin fushinka zai iya wucewa, amma kalmomin da za ka furta cikin fushi, za su tsaya a zuciyar mutanen da ka yi wa furuci cikin fushi har abada. Ba kowane zai iya ba ka uzirin ka yi furucinka cikin fushi ba.

Idan kana cikin fushi, koda wani ya takale ka, ka yi shiru, kar ka yi gaggawar aikata abin da zuciyarka ke ma ƙaiƙayi alhalin kana cikin fushi, fushinka zai iya wucewa, amma abin da ka aikata cikin fushi zai (iya yi) ma illa a gaɓɓanka, ko ga na waninka, ko a mutuncinka ko ga mutuncin waninka, ko ka ɓata mu'amalarka (da wasu mutanen) ta har abada. 

Yawancin saɓani tsakanin abokan zama, ko sakin aure, ana yi ne cikin fushi. Cikin fushi, mata za ta iya haɗa mijinta da iyayenta kan saɓaninsu, amma su (mata da mijinta) su shirya su yafewa juna, amma iyayen na ƙullace da mijin (har abada). Mahaifi ba zai iya tsinewa ɗansa ba sai idan yana cikin fushi. Ubangida ba zai kori yaronsa ba, sai in yana cikin fushi. Fushi kamar maye ne (intoxication), yana iya janyo aikin da-na-sani cikin kiftawar ido.

A halayya, ƙarfi shi ne iya mallakar kai a lokacin fushi (Bukhari, 6114). Shi ya sa Manzon Allah ﷺ Ya koyar, da cewa: "وإذا غضب أحدكم فليسكت". Ma'ana: "Idan ɗayanku ya yi fushi, to ya yi shiru (ya kame)" (Musnad Ahmad, 2135). Idan kana tsaye ka zauna, ka kuma nemi tsarin Allah daga shaiɗan (A'uziyyah) domin fushi kamar maye ne.

✍️Aliyu M. Ahmad
2nd Jumada I, 1444AH
26th November, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari 
#AliMotives

Post a Comment

0 Comments