Ko Kun San

Wata babbar ƙofar da wasu iyayen ke buɗewa 'ya'yansu ta LALACEWA, ita ce, a lokacin da aka kawo ma rahoto, ɗanka ya fara shaye-shaye, (musamman iyaye mata), sai su yi musa, su ƙaryata: "NI ƊANA BA YA SHAYE-SHAYE, SHARRI AKE YI MASA."

Mu fahimta! Shaye-shaye yana da matakai, daga gwadawa (experimentation/first use), zuwa sabawa (regular use), har ya kai matakin da rayuwarsa za ta dogara da shaye-shaye (addiction/dependency).

⚠️ Ji ni da kyau! Ko kai ne ka kai matakin "addiction" a shaye-shaye, aka ce ka bari, wallahi ba ka isa ka daina ba, kuma da wuya mutum yake shiryu, sai dai ikon Allah.

Babban matakin da za ɗauka na kange 'ya'yanka daga shaye-shaye, shi ne, tun farko, ka lura da abokansa, da wurin da yake zama. 

Idan ka sami labarin ɗanka ya fara shaye-shaye kuma, tun yana matakin farko (experimentation), kafin ya zame masa jiki, ka ja shi a jika, ka raba shi da abokan banza (don sune yawanci sila). Amma da zarar ka ƙaryata, cewa yaronka ana ganinsa da ɓatattun yara, shikenan, kamar kun ɗaure masa gindi ne. 

Idan har shaye-shaye ya zame masa jiki, to fa sai dai a yi haƙuri da shi, don ko shi a karan-kansa, bai isa hana kansa "shaye-shaye" ba, ya riga ya zama "addicted", sai an bi matakan "addiction revovery" daga masana, a hankali, tsawon lokaci, idan Allah Ya so shi da shiriya, ya shiryu.

Wannna ke sa wani lokacin, idan yaro ya rasa abin sha, sai ya zama kamar maras lafiya, ko ya faɗi yana burburwa, kamar mai iska, har ana zaton, sihiri ne, ko jinya ko aljannu; NAN KWA SHAYE-SHAYE NE (ya danganta da irin kayan mayen da yake sha [ba zan faɗi "samples" ba!]).

Shi ya sa idan suka yi nisa, duk lokacin da suka rasa abin sha, ba su ƙi su yi sata ba, ko na mene ne, ko kayan wane ne, a siyar kayan, don ya sha kayan maye. Daga shaye-shaye, an ƙara da sata (yaro zama ɓarawo kuma). A wannan matakin, ba zai iya amfanar da kansa ba, ba zai amfanar da waninsa ba, sai jawo magana, da baƙin ciki ga iyayensa da 'yan uwansa, da cutar da mutane da sace-sace, ko koyawa wasu shaye-shaye.

Allah Ya sa mu kula!
Allah Ya shiryar mana da zuri'a.

✍️ 𝗔𝗹𝗶𝘆𝘂 𝗠. 𝗔𝗵𝗺𝗮𝗱
19th Dhul-Qaadah, 1443AH
19th June, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #ShayeShaye #DrugAbuse #AddictionRecovery #Addiction

Post a Comment

0 Comments