Ka yi hankali da 'yan media

Idan ka biya 'yan media, za su kai ka su baro ka, kai ka fi kowa sanin kanka ya kake, ciki da bai, a zahiri.

Ka ga kalmomin Malam, Sheikh... idan aka yaudare ka aka naɗa ma su a ka, ka ɗauka, kake jin kanka a haka, ka sami matsala. Waɗannan a suka ma naɗin nan, su ne dai za su kwance ma, a duk lokacin da ka yi tuntuɓe.

Ka yi mu'amala da kowa, daidai gwargwado, da yawa da kake gani a 'social media' ba wasu ba ne, a zahirin rayuwa, maɗaukaka ne. Wasu kuma da kake ganin su mutane a 'media', a rayuwar zahiri, ƙasƙantattu ne.

Kar ka ruɗu da tara yawan 'likes' da 'comments', ka yi komai da zuciya ɗaya, ka yaɗa kalmominka masu amfani, suna da matuƙar tasiri ga rayuwar mutane da yawa. 

Kaina na yi wa nasiha, da kuma waɗanda za ta amfana. Allah Ya sa mu gama lafiya 🙏 

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments