Sauraron Waƙoƙin Larabawa


Da waƙoƙin Nancy Ajram, Ayed, Asalah, Elissa, Lamjarred... da ta su M. Inuwa, M. Sharif, Ali Jita, Salim Smart duk ɗaya ne, duk waƙoƙin soyayya suke, Hausa da Larabci.


Haka nan da Maher Zain, Sami Yusuf, Kurtis... da Shehu Mai Tajul Izzi, Ambato, Bashir Ɗan Musa.. duk begen Annabi ﷺ suke, bambanci kurum yare ne, Hausa da Larabci.

Kar don kana jin waƙoƙin Larabci kana wa mai jin na Hausa kallon mai saɓo, da Larabci da Hausa duk yare ne. Idan kana kan fahimtar jin waƙa saɓo ne, amma kana jin ta Larabci, in za ka ji waƙarka, kurum ka ji waƙarka, da wacce aka yi da Indiyanci, da ta Korean, da ta Turanci, da ta Hausa, da Larabci, da Swahili duk ɗaya ne.

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments