Da Wayar Hannunka

 



In dai kana da wayar da take iya shiga yanar gizo, you are automatic self-employer sai dai in baka sani ba.


Ya kamata mu fara ginawa kanmu wannan tunanin, a ƙarni na 21 muke, babu buƙatar sai ka jira wani ya taimake ka, ko ya ɗaga (promoting) ka, kai za ka taimaki kanka.


1. A da idan kana son zama ɗan jarida, kana son kana yin rubutu a column, sai ka yi ta bin ƙafa, kana rubutu ana ƙin karɓa. Amma a yau, zaka zama Freelancer, ka nemawa kanka suna, ba tare da lasisi daga kowa ba.


A yau, za ka iya buɗe gidan taka jaridar ONLINE, ka nema mata lasisi, kana aiki daga kan gadonka, cikin ɗakin gidanka, kana samun kuɗin shiga. Daily Nigerian da ire-irensu, misali ne.


• Akwai Google Blogspot da WordPress, duk kyauta ake buɗe su, kuma suna da tsaro sosai.


2. Idan kana da wata baiwa, kake son nuna kwarewa a masana'antar fina-finai, a da sai kana bin directors, producers da manyan 'yan wasa suna wulaƙanta ka, amma a yau za ka iya ƙirƙirar 'content' da zai amfanar da al'umma, ka buɗe channel a social media, ka yi promoting kanka da kanka, kana samun kuɗin shiga. Mu ɗauki misali daga rayuwar Khaby Lame , mai amfani da Tiktok.


• Kana da Podcast, Spotify ... don ka yi promoting na muryarka. 

• Kana da YouTube, TikTok, Instagram, Reels and short videos ... don tallata basirar, cikin videos, kana kuma samin kuɗi.

• Kana da Pinterest, iStock ... don saida hotonka, ko zane-zanenka.

• In ma wallafa littafi za ka yi, baka buƙatar bin wani yana baka wahala, don a ma launching, ga Amazon.eg, Okadabooks ... za ka iya ɗora PDF ana siya, duk duniya, ana biyanka ta wallet har ƙarshen rayuwarka. Ba buƙatar ƙashe kuɗin printing da tara mutane wajen launching.


3. In za ka iya amfani da social media yadda ya kamata, baka buƙatar sai ka buɗe shago, ko ka shiga cikin kasuwa, kana ɗakinka za kana tallata hajarka, ka siyo, ka siyar, ka ci riba. A yi ORDER ka bada a yi DELIVERY. Da haka aka kafa Amazon.com da ire-iren online malls. 


4. Idan ka karanci language (Hausa, Arabic ko English) kana zaune a gida ba aikin yi, yi tunani fara bada Online Tutorial Class(es) a Telegram, Google Classes, ko Clubhouse ko WhatsApp ana biyanka.


Haka, in Islamic Studies kake, akwai littafan addini da za  ka iya haɗa DAURA a kansu, ka samawa kanka kuɗin shiga. Ko ajin koyon ilimin Tajweed ko Qira'a.


Ya kamata mu fara tunani, kuɗin da muke kashewa wajen siyan manyan wayoyin hannu da siyan data kullum ya zama na kamar sa hannun jari ne muke, mai maimakon zame mana liability (nauyi).


Ba ka da sana'a, ba ka da jari, amma kana da wayar hannu ta ƙimarta ta kai 50k+, za ka iya amfani da ita wajen nemawa kanka kuɗin shiga a social media.


Da wayarka za ka iya wallafar basirarka ta Youtube, Tiktok, Blogger, Snapchat, Instagram... ka samawa kanka kuɗin shiga.


✍️Aliyu M. Ahmad

16th Dhul-Hijjah, 1443AH

15th July, 2022CE


#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #FasaharZamani

Post a Comment

0 Comments