NEMAN ILIMIN ADDINI

Neman ilimin addini (ilimin bautawa Allah) WAJIBI ne akan kowane MUSULMI ba ZAƁI ba ne.


Neman ilimi addini ba kamar wani yana son karanta Biology, Engineering, Architecture, Language ko Islamic Studies ba ne a jami'o'i; wannan zaɓi ne. Eh! Ba dole sai kowa ya zama Likita ko Injiniya ba; domin wasu za su ɗaukewa wasu, amma dole ne sai kowa ya yi bauta/ibada. Injiniya sai da ya yi karatun fanonninsa tukun ya zama Injiniya, haka Likita; kai ma dole ka nemi ilimin ibada kafin yinta. 


Ba dole sai kowa ya zama Malami ba, amma dole ne ka nemi ilimin duk wani aiki da motsi da kake da na rayuwa ko wani aiki da sunan addini don kaucewa kuskure da shubuhohi. 


Sanin Ilimin Aqidah (Ma'arifa [sanin Allah] da sanin abubuwan da warware Imani don kauce musu), Sallar nan tun daga tsarki, Azumi, Zakka da Aikin Hajji; Mu'amalar aure da kasuwanci, amana, tausayi da ƙaunar juna dole ne kasan ya ake yinsu a tsarin ilimin addini don kyautata rayuwa. Abin kunya me har yaro ko yarinya su kai munzalin aure, amma ba su da ilimin tsarki balle na mu'amalar aure. Abin kunya ne ka tara ilimin boko amma babu 'Fil' zuwa 'Nasi' a kirjinka, baka iya 'Fatiha' da 'Salatin Annabi ﷺ' ba. Sanin haƙƙoƙin Allah dana Bayinsa (mutane da dabbobi) wajibi ne a kaina da kanku.


Na gani, na kwaikwaya sam ba mafita ba ne, ku nemi ilimin addini ƴan uwa koda da kaɗan-kaɗan ne. Mu yi sani! Sam sam babu wani uzuri cikin jahilci (ma'ana don baka sani ba, baya nufin ba za a ma hisabi a kai ba) [Zaad al-Ma'aad 5/34]. 


Haƙƙi ne akan iyaye da waliyyai bawa ƴaƴa tarbiyya Islamiyya, don in baka san ilimin addinin ba ta yaya zaka bautawa Allah?


Allah Ya sa mu dace, amin.


(c) Aliyu M. Ahmad

26021442AH 14102020CE

Post a Comment

1 Comments