MATASAN YAU DA SOYAYYA
* Soyayya a nan, ina nufin soyayya tsakanin 'saurayi' da 'budurwa'.
Wato har ga Allah, mu matasa (a yau) muna bukatar 'jagoranci' (mentorship) a duk wata gaba ta rayuwarmu. Walau daga iyaye, yayye, malamai ko wasu kwararru da za su rika jibantar lamuranmu.
A lokacin da aka ce (wani) matashi ya fara soyayya, lokacin zai zage dantse wajen nunawa kauna kulawa, ta lokaci, kudi da duk wata dawainiyya ga wacce yake kauna, sam babu zancen nuna gazawa.
Aure dai shi ne burin 'masoya. Amma wannan dawainiyyar da matashi ke yiwa soyayya, takan mantar da shi kan ya fara tanadi zama da masoyiyarsa na har abada (tanadin aure), tunda yana karar da karfinsa da kudinsa a wajen dawaniyya don nuna soyayya.
Zaka ga masoya sun shekara 3 zuwa 5, kowa ya san suna soyayya, cikin unguwa da dangi; amma caraf daya, sai wani (late comer) ya zo cikin 'yan watanni ya aure yarinyar. Saboda an tambayi 'masoyi' an ce ya fito, sai ya ce bai gama shiryawa ba. Shekara 3 - 5, to da duk me ake?
Matashi ya manta cewa, aure yana bukatar tanadi, kudi, gida, kayan aure na al'ada, da kuma bikin aure. Akwai kuma lissafi na rayuwa bayan aure, wanda kullum nauyi ne ke karuwa a kanta.
Ita kuwa mace, 'yar aririta ce, kullum tana bukatar kulawa, kuma ta samu mai bata kulawa kullum. Duk wasu kananan bukatunta nan take yake iya biya mata, kan ka ce kwabo. Wannan ke kulla soyayya mai karfi.
Anan zaka ga, ita mace ga wanda take so, amma ta auri wani daban, ba don bata son saurayinta na farko ba, sai don bai shirya aure ba ne. Su kuma iyaye, maslahar 'yarsu ta isa aure suke dubawa, su bawa wanda ya shirya. Shi ya sa duk da aure nufi ne na Allah, amma DA YAWAN 'YAN MATA, SUNA AUREN WANDA YA SHIRYA NE, BA WANDA SUKE KAUNA BA.
MAFITA:
1. Ta fuskar iyaye: A duk lokacin da danka ya fara zunguru maganar aure, a matsayinka na mahaifi ko waliyyi, ba ido zaka sa masa ba yana abin da ya ga dama ba. A matsayinka na mahaifi, jagoransa a rayuwa, ka zaunar da shi ka tambaye shi, wane irin tanadi yake yiwa abin da yake kokari daukowa?
Idan ka ji wani abu da ba daidai ba, sai ka zame masa fitila. Domin a sha'anin aure, ba'a rufa-rufa, ba'a karya ko yin wani lissafi maras iyuwa.
2. Ta fuskar matashi: Ya kamata idan matashi yana da niyyar aure, ya fara yiwa kansa tanadi.
Misali; a cikin shekaru 3 - 5 na soyayya, ya kamata a ce a kalla kana da miliyan 2 na tanadi da kake yiwa soyayyarku. Domin mallakar gida, da kuma hidimar aure. Ma'ana, misali a kowacce rana inka fita fafutuka, akalla ka iya ajiye #1,000 ko fiye, a kalla shekara kana da #360k zuwa #500k, wannan kawai na tanadi ne.
A sanina, a al'adarmu ba a fiye bawa abin da ya shafi 'feelings' muhimmanci ba, musamman daga wajen manya. Ya kamata ana bawa auren maza muhimmanci, kamar yadda ake bawa na mace, domin dukkaninsu mutane ne. Rayuwar wasu tana shiga garari, ciwon so (psychologically) ciwo ne, yana da wuyar warkewa. Sai ya shafi komai na rayuwar mutum. Irin wannan ke janyo cututtukan kwakwalwa irin su agoraphobia, syngenesophobia,
philophobia sa sauransu.
✍️ Aliyu M. Ahmad
14th Shawwal, 1443AH
15th May, 2022CE
1 Comments
This comment has been removed by the author.
ReplyDelete