FREE ONLINE COURSES: KAI MA ZAKA IYA!

 


KAI MA ZAKA IYA!

Akwai darussa da dama da wasu makarantu, cibiyoyi da kungiyoyi na ƙasashen ƙetare (foreign countries) ke bayarwa kyauta (free), musamma ga ƴan ƙasashe masu tasowa da masu ƙaranci samun kuɗin shiga (low income), kamar Nijeriya.

Bayan wurare da cibiyoyi irin su Coursera, Google, Monash University, Futurelearn, Udacity, Skillshop, AIU, Routers da sauransu, ita ma Metropolitan School of Business & Management, makaranta ce dake London, dake shirya karatuttuka FREE ONLINE (kyauta), a kan abubuwan da suka shafi fasahar kasuwanci, addini, zamantakewar yau, fasahar zamani, fasahar aikin jarida, fasahar rubutu da sauransu.

Ni ma na kammala nawa karatun ‘jiya’ na CREATIVITY AND PROBLEM SOLVING SKILLS, don samun kwarewar yadda za a warware wasu matsalolin, musamma a wannan zamani.

Ga link nan a ƙasa, da zaka iya shiga, domin yin rijista:

https://msbm.edu.ng/programme/free-online-course-in-creativity-and-problem-solving-skills?fbclid=IwAR2tiRggjzxsbHvblkuJvsmw63F-b2xxizp4HkgUn_WmzEWaWQ_k_SK8LkQ

Matakin farko, zaka yi amfani da email naka ka cike bayananka, za su tura ma wani ‘link’ zuwa cikin email naka, sai ka buɗe, ka yi ‘login’, ka fara ɗaukar darasi, cikin ‘video clips’. Bayan ka kammala, zaka yi gwaji (test) na tambayoyi guda 10. Alhamdulillah, a nawa gwajin na samun 100%.

Ba wai iya CERTIFICATES din ba, in ka bada himma, zaka koyi dabarun rayuwa da yawa., musamma da fuskar addini, kasuwanci, fasahar zamani da zamantakewa. Ka yi amfani da 'data'rka da lokacinka, don amfanar da kanka da rayuwar wasu.

Allah Ya bada sa’a.

 

© Aliyu M.Ahmad

2nd September, 2021

Post a Comment

1 Comments