Kana Son Zama Marubuci?


Rubutu (iya sarrafa alƙalami) baiwa ne, kamar yadda iya 'sarrafa harshe' a 'magana' ko 'waƙe/waƙa' yake baiwa, amma duk ana iya koya. Idan kana son zama marubuci, kawai ka fara rubutu, yau, yanzu; ba sai gobe ba.

Duk abin da karanta (na ilimi) ka fahimta, rubuta shi. Duk wata tajriba (experiences) da ka samu a mu'amalar rayuwa, nemi 'dairy', ka rubuta. Babbar asarar marubuci shi ne, ya bar wani ilimi, ko tunani mai kyau ya kuɓuce masa (ya manta) ba tare ya rubuce shi ba.

Idan ka ginu akan ɗabi'ar karatu, lura da rayuwa da kuma rubutu, ilimi ba zai na kuɓuce ma ba. Iya yawan karatunka da rubutunka, iya yawan yadda za ka ƙara ƙaimi wajen son sani sabbin ilimai. Idan kana son zama kwararre (sosai), ka tsayar da alƙalaminka kan iya abin da sani (na ilimi), ban da kutse cikin abin da ba ka da ilimi a kai (sai ka zama, 'jack of all trade, master of none').

Idan kana karantar 'biology', rubuta (iya) abin da kake tunanin zai amfanar, a iya 'biology', haka fannin fasaha, tattali, zamantakewa ko addini. Idan kuma kana da baiwar rubutun fasaha/zube (creative writing) ie. rubutun labari, ko waƙa, wannan ba ya buƙatar fannin ilimi, baiwa ce daga Allah (shi ma ana iya koya, idan kana da sha'awa [passion]). Ana gane baiwar hakan ta hanyar yawan tunanin abin, kuma iya yawan rubuce-rubucenka, iya yadda za ka ƙara samun kwarewa.

Duk yadda kake ji da kanka (a fannin rubutu), ka nemi (wani) mai duba rubutunka (editor), cikin 'yan uwanka, ko abokai da malamanka, ko ma waɗanda za ka biya (da kuɗi) su riƙa duba ma rubutu (freelance editors). Wannan ma yana taimakawa sosai wajen gane kurakurai (cikin rubutu, fahimta ko tunani), tare da samun cike giɓin abubuwan da ba ka sa (a cikin rubutu ba), ko abin da ya dace canja ko cire a cikin rubutu.

✍️Aliyu M. Ahmad
19th Rabi'ul Thani, 1444AH
14th November, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments