Abokiyata ce 🧕🏻


Abokiyata ce 🧕🏻

Ta ce: "Tare muka taso, ƙawata ce tun daga 'primary' har 'senior secondary'.

Gaskiya ba ƙarya Allah ya yi mata halitta, wannan ya sa tun muna ƙanana maza ke bibiyarta suna sonta. Mun shiga SS II, Allah ya ƙaddara ta sami tsayayye aka yi mata aure.

Sai dai ita matsalarta, magana. Tana ɗaukar kanta kamar ita ta shiryawa kanta komai, mu mun kasa yi wa kanmu halitta irin tata. Mun kasa yin farin jini irin nata. Mun kuma ƙi mu yi aure kamar yadda ta yi da wuri. Kullum cikin caka mana magana take da gori, har faɗa suke da sauran schoolmates namu, ni ce ma nake shige mata saboda aminta.

Har dai muka gama WAEC da NECO, duk result namu ya yi kyau sosai. Ni na tafi karatu, ita kuwa mijinta ya ce bai ga amfanin karatunta ba tun dai ta yi aure, ba ta kuma rasa komai ba. Ba zata tafi ƙananan yara da aurenta su kaɗe mata hankali ba, ya san halinta, yana tsoron fitina.

Na gama karatu, na yi NYSC, na sami aiki, na kuma yi aure, a lokacin ni ma bai fi wuce 25 - 26 years ba. Yanzu haka shekara ta 9 da aure, 'ya'yana 3, muna zaune lafiya da mijina, Alhamdulillah!

Darasin da nake son isarwa shi ne, ƙawata aurenta 3, kuma yanzu ma a gida take a zaune. Shi ya sa ka ganni nan, ko ƙannena da yara ba zam bari suna azarɓaɓin kan wata ni'imar da Allah ne ya yi musu, ba su suka yi wa kansu ba sai na gwaɓe su".

Duk da akwai jarrabawa, ni ina ganin akwai harshe, dole mu riƙa kiyayye harshe, mu zama humble cikin al'amuran rayuwar nan.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments