SABBIN FEATURES 12 NA WHATSAPP


Ko kun taɓa kula?

1. 'Admin' na da damar goge 'chats' ko 'attachment' a cikin group. A wajen 'delete', 'admin' zai goge da 'delete for everyone'.

2. Wajen 'attachment' (tura hoto, bidiyo ko file); za iya ƙara 'recipient' (wanda za ka turawa) koda ta cikin 'private chat' ɗin mutum 1 ne.

3. 'In-chat Polls', irin na 'Telegram'. Za ku iya haɗa zaɓe ta cikin Whatsapp, ko kacici-kacici (objectives). Duba wajen attachements 📎, shi ne na ƙarshe (Poll 📊).

4. Za ka iya haɗa 'video call' da mutum 32 ta hanyar 'add participant' a 'video call' ko 'call link'.

5. Za ka tura files mai nauyi 2GB ta Whatsapp.

6. Tsohon feature na 'reactions' da 👍❤️😂😯😢🙏🏻 a kan 'chats' ko 'attachements', ko 'status' ta hanya 'long press' a kan 'chat' ko 'status'.

7. Taƙaita waɗanda za su iya ganinka 'online', kamar yadda ake taƙaita 'status privacy'. Shiga Setting > Privacy Setting > Last See and Online > Who Can See Me My Last See (sai ka 'selecting').

8. Rufe 'screenshot' wajen tura saƙon 'view once'.

9. Ficewa daga group ba tare an san da fitarka ba (sai iya 'admins'), shiga ta 'privacy chat'.

10. 'Review' na voice chat kafin ka tura.

11. Communities, haɗe groups masu manufa a waje ɗaya. Misali: Groups na makaranta, da kowanne departments, levels, da courses (kowanne daban-daban, a folder ɗaya). Duba gefe 'Chats Bar' daga hagu (left), za ga wani 'icon' 👥.

12. Call link, za ka turawa wasu link su joining Whatsapp call (voice ko video). Shiga 'Calls', za ka ga 'Create Call Link' a sama, kafin ka tura, sai ka 'selecting', 'voice call' ko 'video call'.

Yanzu kuma 'Whatsapp' suna aiki a kan chats filters, super group (group da zai iya ɗaukar mutane 100,000 - 1m), companion mode, read later (archive folder)... Idan Whatsapp ɗinka/ki ba shi da waɗancan features da na ambata a sama, yi ƙoƙarin 'updating' ta 'Playstore' (Android) ko 'Appstore' (iPhone).

✍️Aliyu M. Ahmad
22nd Rabi'ul Thani, 1444AH
17th November, 2022CE

Photo Credit: Whatsapp Inc.

#AliyuMAhmad #FasaharZamani #RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments