Addua'a A Ranar Juma'a


Yau Juma'a, akwai wata SA'A da idan mutum ya yi dace yana mai addu'a (roƙon buƙata), Ubangiji zai biya masa buƙatunsa 👇

1. Daga fitowar rana zuwa faduwarta (awa 12 a ranar Juma'a), ko
1. Lokacin huɗuba: tsakanin zaman liman a huɗuba ta farko da ta biyu; ko,
2. Bayan sallar La'asar (a ruwayoyi mafiya rinjaye).

Ranar Juma'a rana ce da ake son:

1. Yawaita zikiri, da 
2. Yawaita Salatin Manzon Allah ﷺ, 
4. Yawaita addu'o'i,
3. Kwaliyya da halartar sallar Juma'a akan lokaci.

Mu sanya ƙasarmu a addu'a, Allah ya ba mu zaman lafiya, da jagorori adalai. Allah Ya kawo mana sauƙin tsadar rayuwa, ya hore mana mu fi ƙarfin buƙatunmu na yau da kullum.

✍️Aliyu M. Ahmad
16th Rabi'ul Awwal, 1444AH
11th November, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #MusuunciDaRayuwa #Jumaat

Post a Comment

0 Comments