Ceto Kai (Self Therapy) Daga Aiyukan Saɓo (Masu Naci) Da Jarababbun Halaye


Ceto kai (self therapy) daga aiyukan saɓo (masu naci) da jarababbun halaye

----------------------------------------------
* Tsakure daga littafin: 
WASIƘA GA MAI KALLON BAT*A
----------------------------------------------

A cikin rubutuna (wancan), na taƙaita bayanai ga ire-iren aiyuka saɓo da halayya (masu naci) da (wasu) mutane ke kasa dainawa, duk da suna da illa ga mutum ta fuskokin addini, lafiya, tattali, sauyin halayya da zamantakewa.

• Na saɓo/alfasha:

1. Alfasha
    a. Nacin kallon bat*a
    b. Zina
    c. Istimna'i [zinar hannu]...
2. Shaye-shaye...

• Na halayya:

3. Nacin amfani da social media (ba don amfani kasuwanci, ko karatu ba)
4. Nacin kallace-kallacen 'films', kwallo ko 'games'
5. Soyayyar wuce iyaka tsakanin saurayi da budurwa
6. Kyamar hallittar jiki, ie. body shaming (wanda ke jawo sanja fata (bleaching), ko shan magungunan ƙara ƙiba)
7. Albozanci... da sauransu.

----------------------------------------------------
* Ba komai ne zan iya rubuta shi, haka a buɗe ba, sai dai a taƙaice (sauran bayanan suna cikin wancan rubutun littafin, insha Allah).
----------------------------------------------------

Idan da gaske kana da niyyar sauyawa, daga wani 'aikin saɓo mai naci' (kallon bat*a, zina, istimna'i), ko wata 'halayya jarababbiyya' (kana cutar da kanka, amma ka kasa dainawa):

1. Nemo biro da takarda
2. Ka zaɓi lokacin da aka fi samun nutsuwa (mis. bayan sallar Asuba, ko Magriba, ko lokacin da ka zo bacci, ko tsakar dare; mis. 2am - 5am)
3. A jikin takardar, ka rubuta sunan wannan saɓon, ko jarabar; ɓaro-ɓaro, sai ka ja layi biyu a tsakiya (ka sa: amfani da rashin amfani)
4. Sai kuma ka rubuta 👇

a. Mene ne matsayin addini kan wannan aikin ko jarabar? 
• Ya dangantakarsa da tattalin arzikinka (kuɗin shiga, sana'a ko kasuwanci) yana rage ma tattali ko himma nema? 
• Ya matsayinsa a zamantakewa (a idon mutane) me ake yawan faɗa a kan ire-iren wannan aikin? 
• Ya dangantakarsa da lafiyarka?
• Yin tunanin yadda yake cinye ma lokaci, maimakon wasu aiyukanka muhimmai.

b. Wane irin amfani wannan aikin yake ba ka a karan kanka? Ko ga mutanen da ke kewaye da kai? Tsakanin amfani da cutarwa, wanne ne ya fi yawa?

Idan ka gama ba wa kanka waɗannan amsoshi, sai (kuma) ka tarar, illolinsa sun fi amfaninsa yawa, a lokacin za ka fara jin tsanar abun, cikin har da jarabar soyayya, nacin kallon film, kwallo, game, social media (fiye da ƙima), bleaching..., zuwa ga manyan aiyukan saɓo: biye-biyen mata, istimna'i, shaye-shaye da kallon alfasha...

Akwai wasu 'maganganu' da Manzon Allah ﷺ ya ambata, cikin hadisai 2, Imam An-Nawawy (631 - 676AH) ya kawo cikin Arba'una, hadisi na 20 da 27:

1. Hadisin Uquba ɗan Amir رضي الله عنه, cewa: "yana daga cikin abin da mutane suka riska na daga cikin maganganun (zantuka) Annabawa farko عليهم السلام cewa: idan ba ka da kunya, to ka yi abin da ka ga dama."

2. Hadisin Nawwas ɗan Sam'an رضي الله عنه, cewa: "Saɓo shi ne abin da yake ma ƙaiƙayi a zuciyarka, kake tsoron mutane su sani".

Sai ka tambayi kanka, me ya sa in zan yi kaza-da-kaza na ke yi ɓoyewa, ko ba na son wani nawa ya sani? Idan zuciyarka tana iya wannan tunanin, haƙiƙa tana raye. Idan kuma mutum ya riga ya yi nisa, har yana iya 'mujahara' (Nathans aikin saɓo), wannan 'therapy' ba na sa ba ne.

Bayan ka gane irin illar da saɓo ko 'wata halayya' ke ma, ta fuskoki da dama, Dr. Abdurrzaƙ cikin "كيف نهرب من الإثم" ya ciro daga "عدة الصابرين وذخيرة الشاكرين" na Ibn Qayyim al-Jawziyyah (691 - 751AH), cewa: (idan aikin saɓo ne) ka yi ƙoƙarin:

1. Tuba na gaskiya, ka tuna za a ma hisabin kan aiyukan saɓo da kake aikatawa.
2. Yin sallar a kan lokaci (cikin jam'i, ga namiji)
3. Yawaita karatun Alƙur'ani, adhkar, da jin karatun.. da barin jin kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe.
4. Ta'amuli da kuɗin halal, abincin halal, suturar halal...halal
5. Ƙauracewa wuraren da ake irin wannan saɓo da shafukan yaɗa su a yanar gizo
6. Maye lokutan da aka saba saɓon da wasu aiyuka na gari (mis. ɗaukar karatu, zikiri, azumin nafila, da zama da mutanen kwarai da ƙauracewa na banza).

✍️ Aliyu M. Ahmad
22nd Rabi'ul Awwal, 1444AH
18th October, 2022CE

#RayuwaDaNazari #AliyuMAhmad

Post a Comment

0 Comments