Phobia


‘Phobia’ shi ne 'matsanin tsoro' ko 'kyamar' wani abu da yake da alaƙa da halayyar mutane, wani lokaci, har wasu kan ganin, mutumin da aka jarraba da ‘phobia’ kamar yana samu ‘shafar shaiɗanu’ (aljannu), ko ‘ragwanci’, ko ‘shaƙiyanci’; wanda ba haka ba ne (a wasu lokutan), daga ciki akwai:

TSORO MAI ALAƘA DA MU’AMALA

1. Philophobia - Tsoron soyayya (kar ka yi mamaki, akwai mutanen da in an ce ana son su (da soyayya), za su shiga firgici, da tsoro, su rikice).

2. Pistanthrophobia - Tsoron gaskatawa ko yarda da mutane.

3. Proditiophobia -  Tsoron da ke sawa mutum tunanin abokin alaƙarsa zai yaudare shi (wannan na jawo yawan zargi tsakanin masoya, ko ma’aurata). 

4. Kakorrhaphiophobia - Tsoron za a yi galaba a kanka, musamman idan ka samu abokin takara a soyayya.

5. Atychiphobia – Tsoron rashin nasara.

6. Thanatophobia – Tsoro mutuwar masoyi, ko soyayya.

7. Androphobia– Tsoron maza

8. Gynophobia – Tsoron mata

9. Venustraphobia – Tsoron Kyakkyawar mace

10. Gamophobia - Tsoron aure

11. Anuptaphobia – Tsoron auren mutumin da bai kamata, ko dace da kai/ke ba.

12. Atelophobia - Tsoron yin kuskure

13. Cacophobia – Tsoron muni

14. Chrometophobia – Tsoron kashe kuɗi

15. Nomophobia – Tsoron zama ba wayar hannu

16. Wiccaphobia – Tsoron sihiri (akwai mutanen da kullum cikin firgici suke, suna tunanin wani ya yi musu asiri, ko zai ƙulla musu sihiri). 

17. Gerascophobia – Tsoron tsufa

18. Hodophobia – Tsoron bulaguro 

19. Anthropophobia/Social phobia - Tsoron mutane

20. Agoraphobia - Tsoron shiga taron mutane

21. Deipnophobia – Tsoron cin abin cikin mutane

22. Chiraptophobia – Tsoron tabawa

TSORO MAI ALAƘA DA HALITTU

23. Musophobia - Tsoron bera

24. Myrmecophobia - Tsoron tururuwa

25. Ailurophobia -  Tsoron kyanwa/kuliya

26. Arachnophobia – Tsoron tattau/gizo-gizo (spider)

TSORON MAI ALAƘA DA JINYA DA YANAYI

27. Hypochondria – Tsoron jinya

28. Nosocomephobia -  Tsoron asibiti

29. Trypanophobia -  Tsoron allura

30. Tokophobia – Tsoron haihuwa

31. Pedophobia -  Tsoron jajiri

32. Traumatophobia – Tsoron jin rauni

33. Nyctophobia – Tsoron duhu

34. Oneirophobia -  Tsoron mafarki

35. Pogonophobia -  Tsoron gemu

36. Tonitrophobia – Tsoron cida/tsawa

37. Monophobia - Tsoron tafiya ko zama cikin kaɗaici (mutum ɗaya)

Kowanne ɗaya daga cikin wa ɗannan ‘phobias’ (da ma wasu), akwai wani sanadin da yake kawo su; wasu saboda sadaniyya faruwar wani abu (mai firgici, rashi, ko tsoro), ko gado (daga iyaye), ko tsoratarwa da wasu iyayen ke yi wa yara ƙanana (mis. tsoratarwa da ‘mage’ ko ‘ɓera’) sai wannan ɗabi’a ta ginu har girmansu. 

Idan kana alaƙa da mutum, musamman mata, idan ta ce na tsoron ‘kuliya’, koda wasa, kar ka tsora ta da ‘kuliya’, akwai waɗanda har ‘suma’ suke idan kuliya ta hau kansu. Akwai waɗanda in an ce za a yi musu ‘aure’ suke ƙi, koda sun sami masu ƙaunarsu da gaske, haka ma ‘soyayya’ (philophobia). 

Idan a gidanku akwai mai wani daga cikin irin waɗannan matsaloli, ku yi ƙoƙarin kai su ga likita (masanin halayya/therapist), wasu na buƙatar ‘shawarwari na ilimi’, wasu kuma haɗe da magunguna.

Babbar kariya ga firgici da tsoro kuma ita ce, lazimtar zikiri a kowanne hali. Idan wani abu da yake ba ka tsoro ya bayyana ma, ka yi tahilili, "LA ILAHA ILLAL-LAH", ko yawaita karanta "اللهم إني أعوذ بك من الهم والحزن والعجز والكسل والجذام والجبن والبخل وأعوذ بك من المأثم والمغرم ومن غلبة الدين وقهر الرجال" (Abu Dawud, 1555).

✍️ Aliyu M. Ahmad
22nd Rabi'ul Awwal, 1444AH
18th October, 2022CE

#RayuwaDaNazari #AliyuMAhmad #Psychology #Phobia

Post a Comment

0 Comments