Yaudara


1. Rataye wani da igiyar soyayya (ta zato), ba da niyyar aure ba (ma’ana, a zuciyarka/ki na da wanda kuke so da gaske, daban),

2. Kasan ‘geno-type’ ɗinka, ba zai iyu ku auri juna ba, sai an yi nisa (a soyayya), ka nuna ku rabu (ko kuma, kana ɗauke da wata cuta da za ta hana aure);

3. ‘Rufa-rufa’, ‘yin ƙarya’, ‘cin amana’ ko ‘zangon-ƙasa’; wanda idan masoyinka ya gano gaskiyar lamari, zai cutu, kuma ƙimarka za ta zube, ko zargi ya shiga tsakaninku (amma a soyayyar gaske).

Manufar soyayya tsakanin namiji da mace, ita ce, AURE [Ibn Majah, 1847]. A ɗabi’a, ba laifi ba ne don ka ga wata/kin ga wani kuna so, mutane ne ku, kowa yana da ‘feelings’ [Adda’u Waddawa’, p. 552].

Sai dai, duk soyayyar da za a gina ta, ba da niyyar aure ba tsakanin masoya:

• Imma za a ɓatawa juna lokaci ne, ko kuma, 
• Ɗaya cikin abokan soyayya na ƙoƙarin yaudarar ɗaya.

Ga namiji! 

A lokacin da Allah Ya ma arziƙin shekaru, ka cika mutum (a halitta), wataƙila har kana da rufin asiri (sana’a, abin hawa, kyakkyawar sutura…) da ka tsayar da ‘yar mutane (budurwa ko bazawara), a tunaninta, ta sami mijin aure ne, mai sonta da gaske; haka iyayenta ma za su yi zato.

Amma:
• Shin da gaske kake son ta, za ka aure ta?
• Ko kuma iyayenka (suna sane), sun amince ka nemi soyayyarta?

Ke kuma kula! 

Ba wai don mutum ya je ya gaida iyayenki shi ke nuna ba yaudara ya zo ba, shin iyayensa sun san da ke?

Iyaye, ba mahaifiyya (mace) ba kaɗai ba, ko 'babbar yayarsa' ba, ko wata ‘aunty’ ba (don kuna gaisawa a waya, ko ya kai ki gare su kun gaisa), a’a; ‘mahaifinsa’, ko wanda yake ‘wakilinsa’ (namiji, babba) sun san da ke?

Irin wannan, idan an ce ya turo iyayensa, zai noƙe, ko fara kame-kame. Akwai kuma wasu, waɗanda daga ƙarshe ma, zai auri wata daban, ya bar ki a igiyar zato. Zai ce “ai a gida ne aka tilasta masa auren wata daban, ba ke ba” ba tare da tun farko kin san da zaman waccar ɗin ba.

Ga mace!

Jo Barnett (2018) a ƙarni na 21, yawanci ‘yan mata, ko ba sa son mutum, ba sa iya fitowa su ambata kai tsaye, cewa; 

• “Ina da wanda nake so” (a yanzu, don kar ka ɓata lokacinka), ko 
• “An min baiko”, da matakamansu.

Wasu kuma, da ka yi Magana, kana son ganin iyayenta, ko a haɗa maganar aure, za ta ce, 

• “ba yanzu ba”
• “a’a, ya yi wuri da yawa...”
• “gaggawar me kake?”

Ɗaiɗaiku ake samu masu faɗa ma gaskiya kai-tsaye (ba sa ra’ayinka) ko su yi wa namiji ‘constructive dismissal’ (kora-da-hali). Wasu (kuma) za su rataye ka, kana zaton kai ɗaya ne, har kana yi wa soyayya bauta, daga ƙarshe, ka ga ‘wedding invitation’, ta ce, “ai a gida ne aka yi mata tilas.”

Idan ba aure ka je nema ba:

1. Ubangiji ﷻ na cewa: 

"وليستعفف الذين لا يجدون نكاحا حتى يغنيهم الله من فضله"

Ma’ana: “Kuma waɗan nan da ba su sami aure ba, su kame kansu, har sai Allah Ya wadatar da su daga falalarSa.” [Nur, aya ta 33].

2. Haramun ne keɓewa da ‘ajanbiyya’*, ko ‘jin daɗin zancenta/hira da ita”… sai idan akwai dalili mai ƙarfi ('aure' ko 'neman aure'):

Imam Al-Akhadary (918AH – 983AH) ya ambata cikin ‘Ahlari’:

"ويحرم عليه... النظر إلى الأجنبية، والتلذذ بكلامها"

* ‘Ajnabiyya’ ita ce macen da ba ta cikin mataye 15 da aka haramtawa namiji aura (Suratul Nisa’i, aya ta 81), ma’ana macen da akwai aure a tsakaninku (budurwa ko bazawara). 

2. Idan aka ce ana sonka/sonki, ba kwa so, ko akwai wanda kuke so daban; yin rataya (zalince ne): nunawa mutum gaskiya ya fi “a clear rejection is better than fake promise” (Bukhari, 5283).

3. Idan kuma an jarabe ka da son wata (da gaske), amma ba ka da halin aure, Manzon Allah ﷺ yana cewa:

"يا معشر الشباب من ...لم يستطع فعليه بالصوم فإنه له وجاء".

“Wanda ba shi da ikon yi)n aure), to,’ lallai ya riƙa azumi don haka shi ne kariyarsa daga zina.‛ [Bukhari, 5066].

Shaykh al-Islam Ibn Taymiyah (661 - 728AH) رحمه الله yake cewa: 

فأما إذا ابتُلى بالعشق وعف وصبر فإنه يثاب على تقواه لله

“Duk wanda aka jarraba da soyayya, in har ya kiyaye mutuncinsa, ya yi haƙuri, Allah zai ba shi ladan wannan...” [مجموع الفتاوى، 10/133].

Idan ka san ba za ka aure ta ba, ko kana da wacce kake so, don me za ka rataye ta? Idan kin san kina da wanda kike so, ko kina da wanda za ki aura, don me za ki karɓi soyayyar wani?

Yaudara daga mace, ko namiji, haramun ce! Domin mayaudari yana siffanta da yawaita ƙarya, cin amana, son zuciya, karya alƙawari… (duk waɗannan suna daga cikin siffofin munafukai). Manzon Allah ﷺ na cewa: "duk wanda ya yaudare mu, ba ya cikinmu (al'ummar Manzon Allah ﷺ)" [Muslim, 147]. 

KAR KA YI ABIN DA, KAI MA IDAN AKA YI MA, ZA KA JI BA DAƊI

✍️ Aliyu M. Ahmad
19th Rabi’ul Awwal, 1444AH
15th October, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Soyayya #Yaudara

Post a Comment

0 Comments