Ba a samun mace tagari A YAU, sai da abin siyan gari (kuɗi). Idan baka da kuɗi, kana ji kana gani wanda ba kalarta ba, bai cancanci auranta ba, zai aure ta, saboda yana da kuɗin ɗaukar ɗawainiyyarta.
A nazarce! Abu ne mai wuya al'umma ta sausata tsada cikin sha'anin aure. Idan kuwa haka ne, SAI A KARƁA A HAKA, ka nemi duk requirements da ake buƙata don ka auri mace tagari.
Tabbas! Aure yana taimakawa sosai wajen ƙange mutum daga faɗawa zinah, amma ba shi ke hana (mutum) zina ba, don akwai (wasu) ma'auratan ma mazinata (wa'iyazubillah). In har za ka yi zina saboda (hujjar) baka da aure, in ka yi auren ma da wuya ka daina.
Allah (SWT) cewa Ya yi, "kuma waɗan nan da ba su sami aure ba, su kame kansu, har sai Allah Ya wadatar da su daga falalarSa.” [Nur, aya ta 33].
A cikin hadisi, Manzon Allah ﷺ Yana cewa: “Ya ku taron samari! Wanda ya samu ikon aure daga cikinku to lallai ne ya yi aure, domin lallai shi ya fi tsarewa daga gani (ido) kuma ya fi tsarewa daga farji. Wanda ba shi da ikon yi, to,’ lallai ya riƙa azumi don haka shi ne kariyarsa daga zina.‛ [Bukhari, 5066].
KA NEMI KUƊI, KA KUMA KAME KANKA KURUM!
✍️ Aliyu M. Ahmad
9th Muharram, 1444AH
7th August, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Aure
Photo Credit: Kartun Muslimah
0 Comments