SIM Card (Subscriber Identity/Identification Module) ma’ana, katin shedar abokan hulɗa ne na gidan waya da ake rabawa mutane lambobin sadarwa (GSM Number) ta ɗaiɗaiku (individual), domin ƙiran waya, ko tura saƙo, ko amfani da data.
An fara yin SIM Card na farko a 1991, girmansa kamar ATM Card, sai Mini/Regular-SIM (1996), sai Micro-SIM (2003), sai Macro-SIM, sai Nano-SIM (2012) sai kuma aka yi eSIM (2016). Amma a Nijeriya sai 2020 aka fara amfani da shi (eSIM).
A Nijeriya, iya layin MTN da 9Mobile ne kaɗai ke amfani da eSIM tunda daga July/August, 2020 har izuwa yau. Kamfanonin Airtel da Glo da sauransu ba su fara amfani da tsarin eSIM ba har yanzu (tukun).
A eSIM, wannan ‘E’ ɗin na nufin ‘EMBEDDED’ ma’ana “wanda aka saka”, yana cikin wayar ne, da shi wayar ta zo, ‘chip’ ne kamar sauran ‘microchips’ na cikin waya. Ana kuma ƙiransa da VIRTUAL SIM ko DIGITAL SIM.
Bambancin eSIM da SIM Card:
1. eSIM ba ya buƙatar sai kana ‘inserting’ da ‘ejecting’ (sakawa da cirewa) a cikin waya, a’a, shi kawai za ka yi ‘logging’ ne kamar email, ta hanyar scanning QR code ko sa lambobi (manually).
2. A eSIM ana iya saving lambobin waya (contacts) sama da 200, ba kamar a SIM Card ba.
3. Ba ka da fargabar faɗuwarsa ko ɓatansa (shi ba sakawa da cirewa ake ba), idan ka sami wata wayar, scanning barcode kawai za ka yi, ko 'logging' da bayananka, ka yi amfani da SIM ɗinka, wajen ƙira, tura saƙo, ko amfani da data.
4. Za a iya ɗora masa layi biyu a wayar da take da slots na SIM guda 2, ko ma fiye (musamman a wayoyin iPhone, ana iya ɗora musu layuka daga 1 zuwa 20 na eSIM).
MALLAKA DA (KUMA) AMFANI DA eSIM
Kafin ka mallaki eSIM ya kamata ka sani:
1. Ba kowacce waya ce take amfani da eSIM ba. Saboda shi eSIM asali a cikin wayar yake (inbuilt ne).
A yanzu, daga cikin wayoyin da suke amfani da eSIM, akwai:
• iPhone daga XR (mai iSO 12.1) zuwa sama; iPhone XR, XS Max, 11, 12 & 13 (Mini, Pro & Pro Max) & SE
• Google Pixel daga Pixel 2 zuwa sama (2, 2XL, 3, 3a, 3XL, 3aXL, 4, 4a, 4XL, 5, 5a, 6, 6a & 6 Pro)
• Samsung: S20 & S1 (Plus [+] & Ultra), Note 20 & 20 Ultra, Fold 3 & Z Flip 3
• Wasu daga cikin wayoyin Huawei (P40 & Mate 40), Oppo (Find X, Reno 6 & A55s), Motorolla Razr da sauransu.
-------------------------------------------
Rukunin wayoyin TECNO, INFINIX da ITEL ba su fara ɗora/amfani da eSIM ba (tukun).
-------------------------------------------
* KA'IDA: Ba za a ma eSIM ba sai an duba wayarka tana da shi, za ta ɗauka tukun a Service Centre (na MTN ko 9Mobile).
2. A yanzu, a Nijeriya, iya layukan MTN da 9Mobile ne ke amfani tsarin eSIM. Za ka je ofishin MTN ko na 9Mobile su ma upgrading (na tsohon layinka) daga SIM Card zuwa eSIM. Za su baka slip mai barcode, SIM Reference number da PUK. KUMA KYAUTA NE (ba a biyan kuɗi)!
3. Bayan ka yi rijista eSIM na tsohon layinka (SIM Card), ko sabon layi, akwai yadda ake ‘activation’ (fara aiki da shi) a waya:
• Android:
Za ka buɗe ‘data’ wayarka, sai ka shiga Setting: > Network and Internet > Mobile Network > Expand Advanced (+) > Carrier > Add Carrier > Download a Sim.
• iPhone/iSO:
Za ka bude ‘data’ wayarka, sai ka shiga: Setting > Cellular > Add a Cellular Plan.
Bayan ka yi downloading (a ƙasa da minti 1), zai buɗe ma ‘QR Scanner’, sai ka ‘scanning’ na ‘QR Code’ na ‘eSIM slip’ da MTN ko 9Mobile suka baka. Ko kuma, ka pressing HELP, zai baka damar sa lambobin da ke jikin ‘eSIM Slip’ da ‘yan gidan waya suka baka. SHIKENAN!
Allah Ya amfana!
✍️Aliyu M. Ahmad
8th Muharram, 1443AH
6th August, 2022CE
#AliyuMAhmad #FasaharZamani #eSIM #BeCyberSmart #MobilePhone
0 Comments