SOYAYYAR MALAMIN ISLAMIYYA

Da farko ya kamata mu fahimta, shi fa malamin Islamiyya ba dutse ba ne, mutum ne mai rai, kamar sauran mutane; yana da ‘feelings’ shi ma, ba laifi ba ne don ya so dalibarsa. 

Ibn Qayyim رحمه الله cikin الداء والدواء a shafi na 552 yake cewa:

" وأما محبّة النِّسْوان فلا لوم على المحِبّ فيها ، بل هي من كماله " .

“Babu laifi don wani (namiji) ya ji yana son wata mace/mata, ba komai/laifi akan wanda yake soyayyar, face ma alamu ne na cikar namiji”.

Duk da haka, akwai abubuwa da ya kamata mu lura da su:

1. A matsayinka na malami, ya kamata ka sani cewa, duk wanda ya zo wajenka karatu, tamkar danka ne, kai ne ubansa mai ba shi tarbiyya. Duk wani abu da zai zubda ma mutunci a wajen ‘ya’yanka ka yi kokarin kiyayewa. 

2. Yawancin abin da yake ja zuciyar malaman islamiyya ga soyayyar daliba, girmamawa da mutuntawa ne.

A matsayinka na mai ilimi, ya kamata ka fahimci mace, don dalibarka tana girmama ka, tana gaisheka a ko’ina, baya nufin tana baka ‘greenlight’ ne; a’a, mata suna da irin wannan dabi’a. Za su iya girmamaka, su yi maka zumunci, amma ba za su iya soyayya da kai ba. 

3. Idan kana malamin islamiyya ka ga dalibarka kana so, in dai da gaske kake, a ka’idar Shari’a, ba zaka fara yiwa ‘mace’ magana ba, ba zaka nemi soyayyarta ba, har sai ka nemi amincewar iyayenta/waliyanta domin baka izinin neman soyayyarta [فقه الحب, p. 19].

4. Soyayya na iya zama jarrabawa! Idan ka nemi soyayyar dalibarka ba ta amince ma ba, ka yi haƙuri, ka dauki hakan a matsayin ƙaddara. Kada ka yi kuskuren zubarwa da kanka mutunci har sauran dalibanka su rainaka saboda soyayya.

Shaykh al-Islam Ibn Taymiyah رحمه الله yake cewa: 

فأما إذا ابتُلى بالعشق وعف وصبر فإنه يثاب على تقواه لله

“Duk wanda aka jarraba da soyayya, in har ya kiyaye mutuncinsa, ya yi hakuri, Allah zai ba shi ladan wannan...” [مجموع الفتاوى، 10/133].

Misalin irin haka ya faru a zamanin Manzon Allah (SAW), a wani hadisin Imam Bukhari (hadisi na 5283), Ibn Abbas ya hakaito labarin Mugheeth mijin Barira (wata ‘yantacciyar baiwar Nana A’isha), cewa, ta kai ga an daura musu aure, amma Barirah ta guji Mugheeth saboda bata son sa.

Mugheeth har kuka yake a cikin mutane saboda soyayyarta. Har wata rana Manzon Allah ﷺ Ya kira ta, yake ce mata “Me yasa ba zaki koma gare shi ba?” Sai ta ce: “Ya Ma’aikin Allah, umarni ne kake ba ni, na koma gare shi?”, Sai ﷺ Ya ce: “A’a, ina son na sasantaku ne kurum.” Sai ta ce: “Tom gaskiya bana son sa.” Sai ﷺ Ya bar ta ta tafi. An ce Mugheeth har ya kare rayuwarsa yana kuka akan soyayyarsa ga Barirah.

6. Gaskiya ana samun wasu daga malaman islamiyya da suke batawa wasu suna, sai ka ga (wani) malami guda yana soyayya da dalibansa ‘yan mata har uku, biyar… a makaranta guda, har a samu wataran suna samun sabani. 

Kuskure ne babba, kuma zalunci ne ka mallake zuciyar mace ba da niyyar aure ba (da yaudara), ko kuma ba halin yin aure a tare da kai. 

Allah (SWT) Yake cewa:

وليستعفف الذين لا يجدون نكاحا حتى يغنيهم الله من فضله

Ma’ana: “Kuma wadan nan da ba su sami aure ba, su kame kansu, har sai Allah Ya wadatar da su daga falalarSa.” [Nur, aya ta 33].

Allah Ya shiryar da mu hanya maidaidaiciyya, amin. 

✍️ Aliyu M. Ahmad 
10th Dhul-Qaadah, 1443AH
10th June, 2022CE

• Photo credit: Anadolu Agency

Post a Comment

0 Comments