#PASSWORD
In ka san 'password' na 'e-mail' naka, lambar wayarka ce, ka yi gaggawar ka canja.
Da iya lambar waya, za a iya bude 'mail' dinka a matsayin 'username' da kuma 'password' lokaci guda.
Misali:
Username: 08012345678
Password: 08012345678
Ko 'e-mail din waye, zai bude. Za kuma a iya shiga kowanne 'shafi' na 'social platforms' da ka bude da wannan 'e-mail' din, ta hanyar "AUTO-FILL."
Ba iya wannan ba, hatta 'history,' 'cookies' na 'browsing' da ka yi, da sauran muhimman bayanai da ke damfare da wannan 'mail' din; duk za a iya bibiya.
Masu sanya saukakenken 'password' a 'e-mail' da sauran 'platforms' an fi sauki 'kwamushe' musu shafukansu cikin sauki.
Irin wannan abubuwa ne masu sauki da ya kamata kowa ya sani. Mu kiyaye, sai Allah Ya kiyaye mu.
(c) Aliyu M. Ahmad
20th Ramadan, 1443AH
21st April, 2022CE
#FasaharZamani
#AliyuMAhmad
1 Comments
We're learning
ReplyDelete