Kana son ka yi kudi?

 


Stephanie Malia Krauss (2018) ta rubuta wata 'muqala' a wata mujallar Amuruka, 'Youth Today' tana cewa, "matasan yanzu sun fi son kudi fiye da damar da zata ba su dama su ci nasara a rayuwa." 


Eh, kusan rayuwar karni na 21 nan, komai kake son yi, sai da kudi. Muhalli, abin ci, sutura, sufuri, ilimi, neman lafiya... Amma kuma a zaharin gaskiya hanyar tara kudi kamar hawa matakalar beni ce, a hankali a hankali a ke yin sama, ba lokaci guda ake tsalle a hau sama ba (Zig Ziglar, 1986).


Kuma ma ka tambayi kanka, duk mutumin da kake kallo yana baka sha'awa, saboda ya mallaki wata kadara ko dukiya, yi tunani, wace irin gwagwarmaya ya sha kafin ya kai ga wannan matakin? In babban ma'aikacin gwamnati ne, kafin ya kai matakin 'director' yana daukar albashi mai tsoka, hawa motocin alfarma; matakai nawa ya taka? Duk wanda ka gani cikin yalwa nema ya yi, ko kuma neman masa aka yi.


Kuma ma ka'idar guda daya ce; Soso Soberekon (2020) a jaridar Legit yake cewa: "shi arziki ba zai zo ma don kawai kai mai addini ba ne; a'a, arziki yana bin mutumin da yake da basira ne, kuma ya yi aiki da wannan basirar. Wannan haka yake ga kowa." Ga mai addini da maras addini, ga mace, ko namiji, ga mutumin kauye ko birni, ga dan talaka ko dan mai rufin asiri... Bahaushe na cewa: "Allah Ya ce tashi in taimake ka."


A cikin Alkur'ani Maigirma, Allah (SWT) yake cewa: فانتشروا في الأرض وابتغوا من فضل الله.." Ma'ana: "ku warwatsu a bayan kasa, ku nema daga falalar Allah..." [Jumaat, aya ta 10]. 


Kuma ko addu'a zaka yi ta neman arziki, ka sani addu'a da aiki kamar tsuntsune mai fukafukai biyu. Dole sai da daya, dayan zai tashi; ba wai zubo ma kudi za a daga sama kamar ruwan damina ba; a'a, kofofin samun arzikin za a bude ma, kai kuma sai zage dantse, ka cire kasala, ka nemi su da baiwarka ko da kasuwanci ta halastacciyar hanya.


Gaggawarmu mu matasa wajen son sai mun yi kudi, son yin bushasha, son a faso gari, son sai mun burge, son sai mun yi suna (shuhura) shi ke kuma jefa da yawa kazamar hanyar neman kudi, ta asiri, kutse (hacking), sata, zamba, cin amana da sauransu. Wasu kwadayi ya sa su zama 'yan farautar 'yan siyasa, ku kashe zuciyarsu, don sun zama 'yan "Allah ya baku ku samu."


Dama da arziki neman ake, ba wai jira ake su zo ba. Ba kuma za kana kwatanta kanka da wanda ya jima a tafiya ba, sannu-sannu a hankali ake isa, ba a gaggawa. “Trees that are slow to grow bear the best fruit.” - Molière (1622-1673).


(c) Aliyu M. Ahmad

2nd Sha'aban, 1443AH

5th March, 2022CE

Post a Comment

0 Comments